Ish 48:17-18
Ish 48:17-18 HAU
Allah Mai Tsarki na Isra'ila, Ubangiji, wanda ya fanshe ku, ya ce, “Ni ne Ubangiji Allahnku, Wanda yake so ya koya muku domin amfanin kanku, Ya kuwa nuna muku hanyar da za ku bi. “Da ma kun kasa kunne ga umarnina kurum! Da sai albarka ta yi ta kwararowa dominku Kamar ƙoramar da ba ta taɓa ƙafewa ba! Da kuma nasara ta samu a gare ku kamar raƙuman ruwa Da suke bugowa zuwa gāɓa.








