YouVersion Logo
Search Icon

Ish 41

41
Alkawarin Allah ga Isra'ila
1Allah ya ce,
“Ku yi shiru ku kasa kunne gare ni, ku manisantan ƙasashe!
Ku yi shiri ku gabatar da ƙararku a ɗakin shari'a.
Za ku sami zarafi ku yi magana.
Bari mu taru mu ga wanda yake da gaskiya.
2“Wane ne wannan da ya kawo mai yin nasara daga gabas,
Ya kuma sa ya ci nasara a dukan inda ya tafi?
Wa ya ba shi nasara a kan sarakuna da al'ummai?
Takobinsa ya sassare su sun zama kamar ƙura!
Kibansa sun warwatsar da su kamar ƙaiƙayi a gaban iska!
3Yana biye da kora, yana kuma tafiya lafiya,
Da sauri ƙwarai, da ƙyar yake taɓa ƙasa!
4Wane ne ya sa wannan ya faru?
Wane ne ya ƙudurta labarun tarihi?
Ni Ubangiji, ina can tun da farko,
Ni kuma Ubangiji Allah,
Zan kasance a can har ƙarshe.
5“Mutanen manisantan ƙasashe suka ga abin da na yi,
Suka tsorata, suka yi rawar jiki saboda tsoro.
Saboda haka duka suka tattaru wuri guda.
6Masu aikin hannu suka taimaka suka ƙarfafa juna.
7Masassaƙi yakan ce wa maƙerin zinariya, ‘A gaishe ka!’
Wanda yake gyara gumaka ya yi sumul
Yana ƙarfafa wanda yake harhaɗa su.
Wani yakan ce, ‘Haɗin ya yi kyau,’
Sukan kuma manne gumakan da ƙusoshi.
8 # 2Tar 20.7; Yak 2.23 “Amma kai, Isra'ila bawana,
Kai ne jama'ar da na zaɓa,
Zuriyar Ibrahim, abokina,
9Na kawo ka daga maƙurar duniya,
Na kira ka daga kusurwoyi mafi nisa.
Na ce maka, ‘Kai ne bawana.’
Ban ƙi ka ba, amma maimakon haka na zaɓe ka.
10Kada ka ji tsoro, ina tare da kai,
Ni ne Allahnka, kada ka bar kome ya firgita ka.
Zan sa ka yi ƙarfi, in kuma taimake ka,
Zan kiyaye ka, in cece ka.
11“Su waɗanda suke fushi da ku, ku jama'ata,
Za a ƙasƙantar da su su ji kunya.
Waɗanda suke faɗa da ku kuwa za su mutu.
12Za ku neme su, amma ba za ku same su ba,
Wato waɗanda suke gāba da ku.
Waɗanda suka kama yaƙi da ku,
Za su shuɗe daga duniya.
13Ni ne Ubangiji Allahnku,
Na ƙarfafa ku, na kuwa faɗa muku,
‘Kada ku ji tsoro, ni zan taimake ku.’ ”
14Ubangiji ya ce,
“Isra'ila, ku kima ne marasa ƙarfi kuma,
Kada ku ji tsoro, zan taimake ku.
Ni Allah Mai Tsarki na Isra'ila, ni ne mai fansarku.
15Zan sa ku zama kamar abin sussuka,
Wanda yake sabo, mai kaushi, mai tsini.
Za ku sussuke duwatsu ku lalatar da su,
Za a marmashe tuddai kamar ƙura.
16Za ku watsa su sama cikin iska,
Iska za ta hure su, ta tafi da su,
Hadiri kuma zai warwatsar da su.
Amma za ku yi murna, gama ni ne Allahnku,
Za ku yabe ni, Allah Mai Tsarki na Isra'ila.
17“Sa'ad da jama'ata ta bukaci ruwa,
Sa'ad da maƙogwaronsu ya bushe da ƙishi,
Sa'an nan ni Ubangiji, zan amsa addu'arsu,
Ni Allah na Isra'ila, ba zan taɓa yashe su ba.
18Zan sa kogunan ruwa su yi gudu daga ƙeƙasassun tuddai,
Maɓuɓɓugan ruwa su yi gudu a kwaruruka.
Zan sa hamada ta zama kududdufan ruwa,
Busasshiyar ƙasa kuma ta zama maɓuɓɓugan ruwa.
19Zan sa itatuwan al'ul su tsiro a hamada,
Da itacen ƙirya, da itacen ci-zaki, da zaitun.
Ƙeƙasasshiyar ƙasa za ta zama kurmi,
Jejin itatuwan fir.
20Mutane za su ga wannan, su sani,
Ni Ubangiji, na yi shi.
Za su fahimta,
Allah Mai Tsarki na Isra'ila ya sa abin ya faru.”
Allah Ya Ce wa Allolin Ƙarya, Ƙalubalanku
21Ubangiji, Sarki na Isra'ila, ya faɗi wannan,
“Ku allolin al'ummai ku gabatar da matsalarku.
Ku kawo dukan gardandamin da kuke da su!
22Ku zo nan ku faɗi abin da zai faru nan gaba,
Ku bayyana wa ɗakin shari'a abubuwan da suka riga sun faru,
Ku faɗa mana yadda zai zama duka,
Domin lokacin da ya faru mu mu sani.
23Ku faɗa mana abin da gaba ta ƙunsa.
Sa'an nan za mu sani, ku alloli ne!
Ku aikata wani abu mai kyau, ko ku kawo wani bala'i,
Ku cika mu da jin tsoro da fargaba!
24Ku da dukan abin da kuke yi ba kome ba ne,
Waɗanda suke yi muku sujada kuwa,
Abin ƙyama ne su!
25“Na zaɓi mutum wanda yake zaune a gabas,
Zan kawo shi don ya kawo hari daga arewa.
Zai tattake masu mulki su zama kamar lāka,
Kamar yadda magini yake tattake yumɓu.
26Wane ne a cikinku ya faɗa mana tun da wuri,
Ko ya yi annabci, cewa wannan zai faru,
Har da za mu ce kun yi daidai?
Ba ko ɗayanku da ya ce tak a kan wannan,
Ba kuwa wanda ya ji kuna faɗar wani abu!
27Ni Ubangiji, ni ne na farko da na faɗa wa Sihiyona albishir,
Na aiki manzo zuwa Urushalima don ya ce,
‘Jama'arki suna zuwa! Suna zuwa gida.’
28Sa'ad da na duba alloli,
Ba wanda yake da abin da zai faɗa,
Ko ɗaya, ba wanda ya iya amsa tambayar da na yi.
29Dukan waɗannan alloli ba su da amfani,
Ba su iya kome ba, ko kaɗan,
Gumakansu ba su da ƙarfi, ba su kuma da iko!”

Currently Selected:

Ish 41: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in