YouVersion Logo
Search Icon

Far 43

43
'Yan'uwan Yusufu Sun Sāke Komawa Masar da Biliyaminu
1A halin yanzu, yunwa ta tsananta a ƙasar. 2Sa'ad da suka cinye hatsin da suka kawo daga Masar, mahaifinsu ya ce musu, “Ku koma, ku sayo mana ɗan abinci.”
3Amma Yahuza ya ce masa, “Mutumin fa, ya yi mana faɗakarwa sosai, ya ce, ‘Idan ba tare da autanku kuka zo ba, ba za ku ga fuskata ba.’ 4In za ka yarda ka aiki ɗan'uwanmu tare da mu, sai mu gangara mu sayo muku abinci. 5Amma idan ba haka ba, ba za mu tafi ba, gama mutumin ya ce mana, ‘Ba za ku ga fuskata ba idan ba ku zo tare da ɗan'uwanku ba.’ ”
6Sai Isra'ila ya ce, “Don me kuka cuce ni, da kuka faɗa wa mutumin nan, kuna da wani ɗan'uwa?”
7Suka amsa, “Ai, mutumin ne ya yi ta tambayar labarinmu da na danginmu, yana cewa, ‘Mahaifinku yana da rai har yanzu? Kuna kuma da wani ɗan'uwa?’ Abin da muka faɗa masa amsoshi ne na waɗannan tambayoyi. Ta ƙaƙa za mu iya sani zai ce, ‘Ku zo da ɗan'uwanku’?”
8Sai Yahuza ya ce wa Isra'ila, mahaifinsu, “Ka sa saurayin a hannuna, mu tashi mu tafi, mu sami abinci mu rayu, kada mu mutu, da mu da kai da ƙanananmu. 9Na ɗauki lamuninsa, a hannuna za ka neme shi. Idan ban komo maka da shi, in kawo shi a gabanka ba, bari alhakin ya zauna a kaina har abada, 10gama da ba don mun yi jinkiri ba, da yanzu, ai, mun yi sawu biyu.”
11Mahaifinsu, Isra'ila ya ce musu, “In tilas haka zai zama, sai ku yi wannan, ku ɗiba daga cikin zaɓaɓɓu, mafiya kyau na albarkar ƙasar a cikin tayakanku, ku kai wa mutumin tsaraba, da ɗan man shafawa na ƙanshi da 'yar zuma, da kayan yaji, da ƙaro, da tsabar citta, da ɓaure. 12Ku ɗauki kuɗi riɓi biyu a hannunku, ku kuma ɗauki kuɗin da aka mayar muku a tayakanku, kila kuskure ne aka yi. 13Ku kuma ɗauki ɗan'uwanku, ku tashi ku sāke komawa wurin mutumin. 14Allah Maɗaukaki ya ba ku tagomashi a gun mutumin, har da zai sakar muku da ɗaya ɗan'uwan nan naku tare da Biliyaminu kuma. Ni kuwa idan na yi rashi, na rasa ke nan.”
15Sai mutane suka ɗauki tsarabar, suka kuma ɗauki riɓin kuɗin a hannunsu tare da Biliyaminu. Suka tashi suka gangara zuwa Masar, suka shiga wurin Yusufu. 16Sa'ad da Yusufu ya ga Biliyaminu tare da su, ya faɗa wa mai hidimar gidansa, ya ce, “Ka shigar da mutanen cikin gida, ka yanka dabba ka shirya, gama mutanen za su ci abincin rana tare da ni.” 17Mutumin kuwa ya yi kamar yadda Yusufu ya faɗa masa, ya shigo da mutanen a gidan Yusufu.
18Mutanen suka tsorata sabili da an kawo su a cikin gidan Yusufu, sai suka ce, “Ai, saboda kuɗin da aka mayar mana cikin tayakanmu a zuwanmu na farko, shi ya sa aka shigar da mu, domin ya nemi hujja a kanmu, ya fāɗa mana, ya maishe mu bayi, ya kuma ƙwace jakunanmu.” 19Sai suka hau wurin mai hidimar gidan Yusufu, suka yi magana da shi a ƙofar gida, 20suka ce, “Ya shugaba, mun zo a karo na farko sayen abinci, 21amma da muka isa zango muka buɗe tayakanmu sai ga kuɗin kowannenmu cif cif bakin taikinsa, don haka ga su a hannunmu, mun sāke komowa da su, 22ga waɗansu kuɗin kuma mun riƙo a hannunmu, mun gangaro mu ƙara sayen abinci. Ba mu san wanda ya sa kuɗin nan namu a tayakanmu ba.”
23Ya amsa ya ce, “Salama na tare da ku, kada ku ji tsoro, Allahnku da Allah na mahaifinku ne kaɗai ya sa muku dukiyar cikin tayakanku. Na karɓi kuɗinku.” Sai ya fito musu da Saminu.
24Da mutumin ya kawo su gidan Yusufu, ya ba su ruwa, suka kuwa wanke ƙafafunsu, sa'an nan kuma ya bai wa jakunansu tauna, 25sai suka shirya tsarabar, domin Yusufu yana zuwa da tsakar rana, saboda sun ji, wai zai ci abinci a nan. 26Sa'ad da Yusufu ya koma gida, suka kawo tsarabar da suka riƙo masa cikin gida, suka sunkuya har ƙasa a gabansa. 27Ya tambayi lafiyarsu ya ce, “Mahaifinku yana lafiya, tsohon nan da kuka yi magana a kansa? Yana nan da rai?”
28Sai suka amsa, “Bawanka, mahaifinmu yana lafiya, har yanzu yana da rai.” Suka sunkuya suka yi masa mubaya'a.
29Sai ya ɗaga idanunsa, ya ga ɗan'uwansa Biliyaminu, ɗan da mahaifiyarsa ta haifa, ya ce, “Wannan shi ne auta naku, wanda kuka yi mini magana a kansa? Allah ya yi maka alheri ɗana!” 30Da Yusufu ya ji kamar zai yi kuka sabili da zuciyarsa tana begen ɗan'uwansa, sai ya gaggauta ya nemi wurin yin kuka. Ya shiga ɗakinsa, a can ya yi kuka. 31Sa'an nan ya wanke fuskarsa, ya fito ya ɗaure, ya umarta a kawo abinci. 32Aka hidimta masa shi kaɗai, su kuma su kaɗai, domin Masarawa ba sukan ci abinci tare da Ibraniyawa ba, gama wannan abin ƙyama ne ga Masarawa. 33Aka zaunar da 'yan'uwan Yusufu a gaban Yusufu bisa ga shekarunsu na haihuwa, daga babba zuwa ƙarami. 'Yan'uwan kuwa suka duddubi juna suna mamaki. 34Daga teburin da yake a gabansa aka riƙa ɗibar rabonsu ana kai musu, amma rabon Biliyaminu ya yi biyar ɗin na kowannensu. Suka kuwa sha, suka yi murna tare da shi.

Currently Selected:

Far 43: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in

YouVersion uses cookies to personalize your experience. By using our website, you accept our use of cookies as described in our Privacy Policy