Eze 4:4-5
Eze 4:4-5 HAU
“Sai kuma ka kwanta a hagunka, ni kuwa zan ɗora maka muguntar Isra'ilawa. Za ka ɗauki muguntarsu bisa ga yawan kwanakin da za ka kwanta a hagunka. Gama na ɗora maka kwanaki bisa ga shekarun muguntarsu, wato kwana ɗari uku da tasa'in da za ka kwanta. Ta haka za ka ɗauki alhakin muguntar mutanen Isra'ila.



