Fit 37
37
Yin Akwatin Alkawari
(Fit 25.10-22)
1Bezalel ya yi akwati da itacen ƙirya, tsawonsa kamu biyu da rabi, fāɗinsa kamu ɗaya da rabi, tsayinsa kamu ɗaya da rabi. 2Ya dalaye shi da zinariya tsantsa ciki da waje, ya kuma yi masa dajiya da zinariya kewaye da shi. 3Ya sa masa ƙawanya huɗu na zinariya a kan kusurwoyinsa huɗu, ƙawane biyu a wannan gefe, biyu kuma a wancan gefe. 4Ya kuma yi sandunan da itacen ƙirya, ya dalaye su da zinariya. 5Sai ya zura sandunan cikin ƙawanen da suke a gyaffan akwatin don ɗaukarsa. 6Ya yi murfin da zinariya tsantsa, tsawonsa kamu biyu da rabi, fāɗinsa kuma kamu ɗaya da rabi. 7Ya kuma ƙera siffofin kerubobi biyu da zinariya, ya maƙala su a gefe biyu na murfin. 8Kerub ɗaya a wannan gefe, ɗaya kuma a wancan gefe. Ya yi su a haɗe da murfin a gefe biyu na murfin. 9Kerubobin suka buɗe fikafikansu sama, suka inuwantar da murfin da fikafikansu. Fuskokinsu kuma na duban juna, suna kuma fuskantar murfin.
Yin Tebur
(Fit 25.23-30)
10Sai kuma ya yi tebur da itacen ƙirya, tsawsonsa kamu biyu, fāɗinsa kamu ɗaya, tsayinsa kamu ɗaya da rabi. 11Ya dalaye shi da zinariya tsantsa, ya yi masa dajiya da zinariya. 12Ya yi masa dajiya mai fāɗin tafin hannu kewaye da shi, ya kuma yi wata dajiya da zinariya kewaye da ita. 13Ya yi wa tebur ɗin ƙawane huɗu na zinariya, ya manna ƙawane a kusurwoyi huɗu na ƙafafunsa. 14Ƙawanen suna kusa da dajiyar inda za a zura sanduna na ɗaukar teburin. 15Ya yi sanduna da itacen ƙirya don ɗaukar teburin. Sa'an nan ya dalaye su da zinariya. 16Ya yi kayan teburin da zinariya tsantsa, wato farantansa, da kwanonin tuya, da kwanoninsa, da butoci domin yin hadaya ta sha.
Yin Alkuki
(Fit 25.31-40)
17Ya yi alkuki da zinariya tsantsa. An yi gindinsa da gorar jikinsa da ƙerarriyar zinariya. Ƙoƙunan alkukin da mahaɗansa, da furanninsa, a haɗe aka yi su da alkukin. 18Akwai rassan fitila guda shida, uku a wannan gefe, uku kuma a wancan. 19A kowane reshe na alkukin akwai ƙoƙuna uku masu kamar tohon almond, akwai kuma mahaɗai da furanni. 20A bisa alkukin kuma akwai ƙoƙuna guda huɗu da aka yi su kamar tohon almond, da mahaɗai, da furanni. 21Akwai mahaɗi kuma a ƙarƙashin kowane reshe biyu biyu na dukan rassan guda shida, a miƙe daga alkukin. 22An ƙera mahaɗai da rassan alkuki a haɗe. Da ƙerarriyar zinariya aka yi alkukin da dukan kome nasa a haɗe. 23Da zinariya tsantsa ya yi fitilu bakwai, da hantsuka da farantansa. 24Da zinariya tsantsa na talanti ɗaya ya yi alkukin da kayayyakinsa duka.
Yin Bagaden Ƙona Turare
(Fit 30.1-5)
25Ya yi bagaden ƙona turare da itacen ƙirya, tsawonsa kamu ɗaya, fāɗinsa kamu ɗaya, shi murabba'i ne, tsayinsa kuma kamu biyu ne, zankayensa kuwa a haɗe suke da shi. 26Ya dalaye shi da zinariya tsantsa, da bisansa, da kewayen gyaffansa, da zankayensa. Ya kewaye shi kuma da dajiya ta zinariya. 27Ya sa masa ƙawane biyu na zinariya a gyaffansa a ƙarkashin dajiya daura da juna don a zura sandunan ɗaukarsa. 28Ya kuma yi sanduna biyu da itacen ƙirya, sa'an nan ya dalaye su da zinariya.
Yin Man Keɓewa da Turare
29 #
Fit 30.22-38
Ya yi tsattsarkan mai na keɓewa da kuma turare mai ƙanshi yadda mai yin turare yakan yi.
Currently Selected:
Fit 37: HAU
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979

: