Fit 34
34
Allunan Dutse na Biyu
(M.Sh 10.1-5)
1Ubangiji ya ce wa Musa, “Sassaƙa alluna biyu na dutse kamar na farkon, ni kuwa in rubuta kalmomin da suke cikin alluna na farko da ka farfasa. 2Da safe ka shirya, ka zo Dutsen Sina'i ka gabatar da kanka gare ni a kan dutsen. 3Kada wani mutum ya zo tare da kai, kada a ga kowane mutum a ko'ina a kan dutsen, kada a bar garkunan tumaki, da na awaki, da na shanu su yi kiwo kusa da dutsen.” 4Sai Musa ya sassaƙa alluna biyu na dutse kamar na farko, ya tashi da sassafe, ya hau Dutsen Sina'i, kamar yadda Ubangiji ya umarce shi. Ya riƙe allunan nan biyu na dutse a hannunsa. 5Ubangiji kuwa ya sauko cikin girgije ya tsaya tare da shi a can, ya yi shelar sunansa.
6 #
Fit 20.5,6; L.Ƙid 14.18; M.Sh 5.9,10; 7.9,10 Ya kuma gifta a gaban Musa, ya ce, “Ni ne Ubangiji, Ubangiji Allah mai jinƙai, mai alheri, mai jinkirin fushi, mai yawan ƙauna, mai gaskiya. 7Ni ne mai nuna ƙauna ga dubbai, mai gafarta mugunta, da laifi, da zunubi, wanda ba zai kuɓutar da mai mugunta ba, amma saboda laifin iyaye nakan hukunta 'ya'ya da jikoki har tsara ta uku da ta huɗu.”
8Sai Musa ya hanzarta, ya sunkuyar da kansa ƙasa, ya yi sujada. 9Ya ce, “Idan na sami tagomashi a gare ka, ya Ubangiji, ina roƙonka, ka yi tafiya tare da mu, ko da yake jama'a masu taurinkai ne, ka gafarta laifinmu, da zunubinmu, ka sa mu zama abin gādonka.”
Sabunta Alkawari
10Allah kuwa ya ce, “Ga shi, na yi alkawari, cewa a gaban dukan jama'a zan aikata al'ajabai irin waɗanda ba a taɓa aikatawa a duniya ba, ko cikin wata al'umma. Dukan mutanen da kuke zaune tare da su za su ga aikina, gama zan aikata abin bantsoro a cikinku. 11Ku kiyaye abin da na umarce ku a wannan rana. Ga shi, zan kora muku Amoriyawa, da Kan'aniyawa, da Hittiyawa, da Ferizziyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa. 12Ku fa kula da kanku, kada ku kuskura, ku ƙulla alkawari da mazaunan ƙasar inda za ku tafi, don kada su zama muku alƙalai. 13#M.Sh 16.21 Sai ku rurrushe bagadansu, ku farfashe al'amudansu, ku sassare gumakansu.
14“Ba za ku yi wa wani allah sujada ba, sai dai ni, gama sunana Mai Kishi, gama ni Allah mai kishi ne. 15Kada ku ƙulla alkawari da mazaunan ƙasar don kada sa'ad da suke shagulgulan bidi'arsu ga allolinsu, suna miƙa musu hadaya, waninsu ya gayyace ku ku ci abin hadayarsa. 16Kada kuma ku auro wa 'ya'yanku maza 'yan matansu 'ya'ya matansu kuma su yi shagulgulan bidi'ar allolinsu, har su sa 'ya'yanku su bi allolinsu.
17 #
Fit 20.4; L.Fir 19.4; M.Sh 5.8; 27.15 “Kada ku yi wa kanku alloli na zubi.
18 #
Fit 12.14-20; L.Fir 23.6-8; L.Ƙid 28.16-25 “Sai ku kiyaye idin abinci marar yisti har kwana bakwai a ƙayyadadden lokacinsa a watan Abib, gama a watan Abib kuka fito Masar. A lokacin za ku ci abinci marar yisti kamar yadda na umarce ku.
19 #
Fit 13.2
“Kowane ɗan farin mutum, ko na dabba nawa ne, duk da 'ya'yan farin dabbobinku, wato ɗan farin saniya da na tunkiya. 20#Fit 13.13 Ɗan farin jaki kuwa za ku fansa da ɗan rago, in kuwa ba za ku fansa da ɗan rago ba, sai ku karya wuyansa. Za ku fanshi kowane ɗan fari. Kada a sami wanda ya zo gabana hannu wofi.
21 #
Fit 20.9,10; 23.12; 31.15; 35.2; L.Fir 23.3; M.Sh 5.13,14 “Cikin kwana shida za ku yi aiki, amma a kan rana ta bakwai sai ku huta, ko lokacin noma ne, ko lokacin girbi sai ku huta.
22 #
L.Fir 23.15-21; L.Ƙid 28.26-31;
L.Fir 23.39-43
“Ku kuma kiyaye idin mako, wato idin girbin nunan fari na alkama, da idin gama tattara amfanin gonaki a ƙarshen shekara.
23“Sau uku cikin shekara mazajenku duka za su hallara a gabana, ni Ubangiji Allah na Isra'ila. 24Gama zan kori al'ummai daga gabanku, in fāɗaɗa kan iyakarku. Ba wanda zai yi ƙyashin ƙasarku a lokatan nan uku na shekara da kukan hallara a gaban Ubangiji Allahnku.
25 #
Fit 12.10
“Ba za ku miƙa jinin hadayata tare da abinci mai yisti ba, kada kuma a bar hadaya ta Idin Ƙetarewa ta kwana.
26 #
M.Sh 26.2;
M.Sh 14.21
“Sai ku kawo nunan farin amfanin gonarku a cikin gidan Ubangiji Allahnku.
“Kada ku dafa ɗan akuya da madarar uwarsa.”
27Ubangiji ya kuma ce wa Musa, “Rubuta waɗannan kalmomi, gama daidai suke da kalmomin alkawarin da suke tsakanina, da kai, da Isra'ila.” 28Musa kuwa yana tare da Ubangiji yini arba'in da dare arba'in, bai ci ba, bai sha ba. Sai ya rubuta kalmomin alkawarin a kan allunan, wato dokokin nan goma.
Musa Ya Sauko daga Dutsen
29 #
2Kor 3.7-16
Sa'ad da Musa ya sauko daga Dutsen Sina'i da alluna biyu na alkawarin a hannunsa, ashe, bai sani ba, amma fuskarsa tana annuri saboda zaman da ya yi a gaban Ubangiji. 30Sa'ad da Haruna da dukan jama'ar Isra'ila suka ga fuskar Musa tana annuri, suka ji tsoro su kusace shi. 31Sai Musa ya kirawo Haruna tare da shugabannin jama'ar duka, suka zo wurinsa, shi kuwa ya yi magana da su. 32Daga nan jama'ar Isra'ila duka suka matsa kusa, Musa kuwa ya ba su dukan dokoki waɗanda Ubangiji ya ba shi a bisa Dutsen Sina'i. 33Da Musa ya gama magana da su, sai ya lulluɓe fuskarsa. 34Amma duk lokacin da ya je gaban Ubangiji domin ya yi magana da shi, sai ya kware lulluɓin, har lokacin da ya fito. Idan ya fito, sai ya faɗa wa jama'ar Isra'ila abin da aka umarce shi. 35Jama'ar Isra'ila kuwa sukan ga fuskar Musa tana annuri. Sa'an nan Musa ya sāke lulluɓe fuskarsa, har lokacin da ya shiga don ya yi magana da Ubangiji.
Currently Selected:
Fit 34: HAU
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979

: