Fit 27:20-21
Fit 27:20-21 HAU
“Sai a umarci Isra'ilawa su kawo tsabtataccen man zaitun tatacce domin fitilar. Za a kunna fitilar ta yi ta ci koyaushe. Za a ajiye ta a cikin alfarwar a gaban labule na wurin shaida. Haruna da 'ya'yansa za su lura da ita daga safiya har maraice. Wannan zai zama ka'ida har abada ga Isra'ilawa.”



