YouVersion Logo
Search Icon

Fit 10:21-23

Fit 10:21-23 HAU

Sa'an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Miƙa hannunka sama, domin a yi duhu cikin ƙasar Masar, irin duhun da za a iya taɓawa.” Sai Musa ya miƙa hannunsa sama, aka kuwa yi duhu baƙi ƙirin har kwana uku a dukan ƙasar Masar. Mutum bai iya ganin ɗan'uwansa ba, ba kuma mutumin da ya iya fita gidansa har kwana uku. Amma akwai haske inda Isra'ilawa suke zaune.