Fit 10:13-14
Fit 10:13-14 HAU
Sai Musa ya miƙa sandansa bisa ƙasar Masar, Ubangiji kuwa ya sa iskar gabas ta hura a ƙasar dukan yini da dukan dare, har safiya. Iskar gabas ɗin kuwa ta kawo farar. Farar ta mamaye ƙasar Masar, ta rufe dukan ƙasar. Ba a taɓa ganin fara ta taru da yawa kamar haka ba, ba kuwa za a ƙara ganin kamar haka ba.





