Esta 9
9
Yahudawa Sun Hallaka Maƙiyansu
1A kan rana ta goma sha uku ga watan sha biyu, wato watan Adar, a ranar da za a aikata maganar sarki da dokarsa, wato a ranar da maƙiyan Yahudawa za su fāɗa musu, sai ranar ta zama ranar da Yahudawa ne za su tasar wa maƙiyansu. 2Sai Yahudawa suka taru a biranensu a dukan lardunan sarki Ahasurus, don su tasar wa waɗanda suke so su yi musu ɓarna. Ba wanda ya tasar musu gama tsoronsu ya kama mutane. 3Dukan sarakunan larduna, da hakimai, da masu mulki, da ma'aikatan sarki, suka taimaki Yahudawa, gama tsoron Mordekai ya kama su. 4Gama Mordekai ya zama babban mutum a gidan sarki, ya kuma yi suna a dukan larduna, gama ya yi ta ƙasaita gaba gaba. 5Yahudawa kuwa suka kashe dukan maƙiyansu da takobi. Suka hallaka maƙiyansu yadda suke so.
6A Shushan, masarauta kanta, Yahudawa suka hallaka mutum ɗari biyar. 7Suka kuma kashe Farshandata, da Dalfon, da Asfata, 8da Forata, da Adaliya, da Aridata, 9da Farmashta, da Arisai, da Aridai, da Waizata. 10Su ne 'ya'ya goma na Haman, ɗan Hammedata, maƙiyin Yahudawa, amma ba su washe dukiyarsu ba.
11A ranar ce aka faɗa wa sarki yawan mutanen da aka kashe a Shushan, masarauta. 12Sai sarki ya ce wa sarauniya Esta, “A Shushan, masarauta, Yahudawa sun kashe mutum ɗari biyar da kuma 'ya'yan Haman guda goma. Mene ne suka yi a sauran lardunan sarki? Mece ce kuma bukatarki? Za a yi miki. Mene ne kuma roƙonki? Za a ba ki.”
13Esta ta ce, “Idan sarki ya yarda, bari a yardar wa Yahudawan da suke Shushan su yi haka gobe, kamar yadda suka yi yau. Bari a rataye gawawwakin 'ya'yan Haman guda goma a bisa gumagumai.” 14Sarki kuwa ya ce a yi haka ɗin. Sai aka yi doka a Shushan, aka kuwa rataye gawawwakin 'ya'yan Haman guda goma. 15Yahudawan da suke Shushan kuwa suka taru a rana ta goma sha huɗu ga watan Adar, suka kashe mutum ɗari uku a Shushan, amma ba su washe dukiyarsu ba.
Bikin Furim
16Yahudawan da suke cikin lardunan sarki kuma suka taru, suka kare rayukansu, suka ƙwaci kansu daga maƙiyansu. Suka kashe mutum dubu saba'in da dubu biyar (75,000) daga cikin maƙiyansu, amma ba su washe dukiyarsu ba. 17A rana ta goma sha uku ga watan Adar ne suka aikata wannan abu. A rana ta goma sha huɗu suka huta, suka mai da ranar ta zama ta biki, da farin ciki. 18Amma Yahudawan da suke a Shushan suka taru a rana ta goma sha uku, da rana ta goma sha huɗu, suka huta ran goma sha biyar, suna biki da murna. 19Yahudawan da suke zaune a ƙauyuka, da karkara, suka mai da rana ta goma sha huɗu ga watan Adar, ranar farin ciki, da biki, da hutu, da ranar aika wa juna da abinci.
20Mordekai kuwa ya rubuta abubuwan nan da suka faru, ya aika da takardun zuwa ga dukan Yahudawa waɗanda suke a dukan lardunan sarki Ahasurus, na kusa da na nesa. 21Ya yi musu umarni, cewa su kiyaye rana ta goma sha huɗu da ta goma sha biyar na watan Adar a kowace shekara. 22Su ne ranakun da Yahudawa suka sami kuɓuta daga abokan gābansu. A wannan wata ne kuma baƙin cikinsu ya zama farin ciki, makokinsu kuma ya zama hutawa. Sai su maishe su ranakun biki da farin ciki, da aika wa juna da abinci, da kuma ba da kyautai ga matalauta. 23Sai Yahudawa suka ɗauka su yi kamar yadda suka fara, da kuma yadda Mordekai ya rubuta musu.
24Haman Ba'agage, ɗan Hammedata, maƙiyin dukan Yahudawa, ya ƙulla wa Yahudawa makirci don ya hallaka su. Ya jefa Fur, wato kuri'a don ya hallaka su. 25Amma da Esta ta zo wurin sarki, sai sarki ya ba da umarni a rubuce, cewa mugun makircin nan da Haman ya shirya wa Yahudawa ya koma a kansa. Shi da 'ya'yansa maza aka rataye su a bisa gumagumai. 26Saboda haka suka sa wa ranakun nan suna Furim, wanda asalinsu daga Fur ne, wato kuri'a. Domin haka dukan abin da aka rubuta a wannan takarda, da abin da suka gani a wannan al'amari, da abin da ya same su, 27sai Yahudawa suka ga wajibi ne a gare su, da zuriyarsu, da waɗanda ka tare da su, su kiyaye ranaku biyu ɗin nan ba fashi kowace shekara, bisa ga abin da aka rubuta. 28Za a tuna da ranakun nan, a kiyaye su a kowane zamani, da kowane iyali, da lardi, da birni. Ranakun Furim ɗin nan, Yahudawa ba za su daina tunawa da su ba, zuriyarsu kuma ba za ta daina tunawa da su ba.
29Sa'an nan sarauniya Esta 'yar Abihail, da Mordekai Bayahude, ta ba da cikakken iko a rubuce don ta tabbatar da takardan nan ta biyu game da Furim. 30Aka aika da takardun zuwa ga dukan Yahudawa da suke a lardi ɗari da ashirin da bakwai na mulkin Ahasurus, da kalmomin salama da na gaskiya, 31da cewa a kiyaye ranakun Furim a lokacinsu, kamar yadda Mordekai Bayahude, da sarauniya Esta, suka umarci Yahudawa, kamar yadda kuma suka kafa wa kansu da zuriyarsu lokacin tunawa da azuminsu da baƙin cikinsu. 32Da umarnin Esta aka kafa ka'idodin Furim, aka kuwa rubuta su a littafi.
Currently Selected:
Esta 9: HAU
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979

: