Afi 4:14-15
Afi 4:14-15 HAU
An yi wannan kuwa don kada mu sāke zama kamar yara, waɗanda suke jujjuyawa, iskar kowace koyarwa tana ɗaukar hankalinsu, bisa ga wayon mutane da makircinsu da kissoshinsu. A maimakon haka, sai mu faɗi gaskiya game da ƙauna, muna girma a cikinsa ta kowace hanya, wato Almasihu, shi da yake shugabanmu.





