YouVersion Logo
Search Icon

M.Sh 6

6
Babban Umarni
1“Waɗannan su ne umarnai, da dokoki, da farillai waɗanda Ubangiji Allahnku ya umarce ni in koya muku domin ku kiyaye su a ƙasar da kuke hayewa zuwa ciki don ku mallake ta, 2don ku ji tsoron Ubangiji Allahnku, ku da 'ya'yanku da jikokinku, ku kuma kiyaye dukan dokokinsa da umarnansa, waɗanda nake umartarku dukan kwanakinku don ku yi tsawon rai. 3Don haka, ku ji, ya Isra'ilawa, ku lura, ku kiyaye su domin zaman lafiyarku, domin kuma ku riɓaɓɓanya ƙwarai a ƙasar da take mai yalwar abinci yadda Ubangiji Allah na kakanninku ya alkawarta muku.
4 # Mar 12.29 “Ku ji, ya Isra'ilawa, Ubangiji shi ne Allahnmu, Ubangiji ɗaya ne. 5#Mat 22.37; Mar 12.30; Luk 10.27 Sai ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku da zuciya ɗaya, da dukan ranku, da dukan ƙarfinku. 6#M.Sh 11.18-20 Waɗannan kalmomi da na umarce ku da su a yau, za su zauna a zuciyarku. 7Sai ku koya wa 'ya'yanku su da himma. Za ku haddace su sa'ad da kuke zaune a gida, da sa'ad da kuke tafiya, da sa'ad da kuke kwance, da sa'ad da kuka tashi. 8Za ku ɗaura su a hannunku da goshinku don alama. 9Za ku kuma rubuta su a madogaran ƙofofin gidajenku, da ƙofofinku.”
Faɗakarwa a kan Rashin Biyayya
10 # Far 12.7; Far 26.3; Far 28.13 “Sa'ad da Ubangiji Allahnku ya kai ku ƙasar da ya rantse wa kakanninku Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, zai ba ku manyan birane masu kyau waɗanda ba ku ne kuka gina ba, 11da gidaje cike da abubuwa masu kyau waɗanda ba ku ne kuka cika su ba, da rijiyoyi waɗanda ba ku ne kuka haƙa ba, da gonakin inabi da itatuwan zaitun waɗanda ba ku ne kuka dasa ba. Sa'ad da kuka ci, kuka ƙoshi, 12to, kada ku manta da Ubangiji wanda ya fito da ku daga ƙasar Masar, daga gidan bauta. 13#Mat 4.10; Luk 4.8 Sai ku ji tsoron Ubangiji Allahnku. Shi ne za ku bauta masa, ku rantse da sunansa. 14Kada ku bi waɗansu alloli na al'umman da suke kewaye da ku, 15gama Ubangiji Allahnku wanda yake zaune a tsakiyarku, mai kishi ne, don kada Ubangiji Allahnku ya husata, ya shafe ku daga duniya.
16 # Mat 4.7; Luk 4.12; Fit 17.1-7 “Kada ku gwada Ubangiji Allahnku kamar yadda kuka yi a Masaha. 17Sai ku himmantu ku kiyaye umarnan Ubangiji Allahnku, da farillansa, da dokokinsa waɗanda ya umarce ku da su. 18Sai ku yi abin da yake daidai, da abin da yake mai kyau a gaban Ubangiji saboda lafiyarku, domin kuma ku shiga ku mallaki ƙasa mai kyau wadda Ubangiji ya rantse zai ba kakanninku. 19Zai kuwa kori maƙiyanku a gabanku kamar yadda ya alkawarta.
20“Idan nan gaba 'ya'yanku suka tambaye ku ma'anar maganarsa, da dokoki, da farillai, waɗanda Ubangiji Allahnmu ya umarce ku da su, 21sai ku amsa wa 'ya'yanku, ku ce, ‘Dā mu bayin Fir'auna ne a ƙasar Masar, amma Ubangiji ya fisshe mu daga Masar da dantse mai iko. 22A idonmu Ubangiji ya aikata manyan alamu masu banmamaki, da mu'ujizai gāba da Masarawa, da Fir'auna, da dukan gidansa. 23Ya fisshe mu daga wurin, ya bi da mu zuwa ƙasar da ya alkawarta wa kakanninmu zai ba mu. 24Ubangiji kuwa ya umarce mu mu kiyaye dukan waɗannan umarnai, mu kuma ji tsoron Ubangiji Allahnmu domin amfanin kanmu kullum, domin kuma mu wanzu kamar yadda muke a yau. 25Idan mun lura, muka kiyaye waɗannan umarnai, muka aikata su kamar yadda Ubangiji Allahnmu ya umarce mu, zai zama adalci a gare mu.’ ”

Currently Selected:

M.Sh 6: HAU

Highlight

Copy

Compare

Share

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in