M.Sh 21
21
Yadda za a yi da Laifin Kisankai da ba a San wanda ya yi Ba
1“Idan aka iske gawar mutum wanda wani ya kashe a fili a ƙasar da Ubangiji Allahnku ya ba ku, ku mallaka, ba a kuwa san wanda ya kashe shi ba, 2sai dattawanku da alƙalanku su fito su auna nisan wurin daga gawar zuwa garuruwan da yake kewaye da gawar. 3Dattawan garin da ya fi kusa da gawar za su ɗauki karsana wadda ba a taɓa aiki da ita ba, ba a kuma taɓa sa mata karkiya ba. 4Sai dattawan garin nan su kai karsanar kwari inda ruwa yake gudu, inda ba a taɓa noma ko shuka ba. A can cikin kwarin za a karya wuyan karsanar. 5Sa'an nan sai firistoci, 'ya'yan Lawiyawa, su fito gaba, gama su ne Ubangiji Allahnku ya zaɓa don su yi masa aiki, su sa albarka da sunansa, su ne kuma masu daidaita kowace gardama da cin mutunci. 6Sai dukan dattawan garin da ya fi kusa da gawar su wanke hannuwansu a bisa karsanar da aka karya wuyanta a kwarin. 7Sa'an nan su ce, ‘Hannuwanmu ba su zub da wannan jini ba, idanunmu kuma ba su ga wanda ya zubar da shi ba. 8Ya Ubangiji, ka kuɓutar da jama'arka, Isra'ila, wadda ka fansa, kada ka bar alhakin jinin marar laifin nan ya kama jama'arka, Isra'ila. Ka gafarta musu alhakin wannan jini.’ 9Ta haka za ku kawar da alhakin jinin marar laifi daga cikinku, sa'ad da kuka yi abin da yake daidai a wurin Ubangiji.”
Yadda Za a Yi da Matan da Aka Kama Wurin Yaƙi
10“Sa'ad da kuka tafi yaƙi da magabtanku, Ubangiji Allahnku kuwa ya bashe su a hannunku, kun kuwa kama su bayi, 11in a cikinsu ka ga wata kyakkyawar mace wadda ka yi sha'awarta, to, ka iya aurenta. 12Sai ka kawo ta gidanka, ta aske kanta, ta yanke farcenta, 13ta tuɓe tufafin bauta. Sa'an nan sai ta zauna a gida tana makokin mahaifinta da mahaifiyarta har wata ɗaya cif. Bayan haka ka iya shiga wurinta, ka zama mijinta, ita kuma ta zama matarka. 14In ka ji ba ka bukatarta, sai ka sake ta ta tafi inda take so, amma kada ka sayar da ita, kada kuma ka wahalshe ta, tun da yake ka riga ka ƙasƙantar da ita.”
Ka'ida a kan Gādon Ɗan Fari
15“Idan mutum yana da mata biyu, amma ya fi ƙaunar ɗayar, idan kuwa dukansu biyu, wato mowar da borar, suka haifi 'ya'ya, idan bora ce ta haifi ɗan fari, 16to, a ranar da zai yi wa 'ya'yansa wasiyya a kan gādon da zai bar musu, kada ya sa ɗan mowa ya zama kamar shi ne ɗan fari, a maimakon ɗan borar wanda shi ne ɗan farin, 17Amma sai ya yarda ya ba ɗan farin, wato ɗan borar, za a ba shi riɓi biyu na dukan abin da yake da shi gama shi ne mafarin ƙarfinsa, yana da hakkin ɗan fari.”
Gagararren Ɗa
18“Idan mutum yana da gagararren ɗa wanda ba ya jin maganar mahaifinsa da ta mahaifiyarsa, sun kuma hore shi, duk da haka bai ji ba, 19sai mahaifinsa da mahaifiyarsa su kama shi, su kawo shi wurin dattawan garin a dandalin ƙofar gari. 20Sai su faɗa wa dattawan garinsu, su ce, ‘Wannan ɗanmu ne, gagararre, ba ya yi mana biyayya. Shi mai zari ne, mashayi!’ 21Sa'an nan, sai mutanen garin su jajjefe shi da duwatsu har ya mutu. Ta haka za ku kawar da mugunta daga cikinku. Dukan Isra'ilawa za su ji, su ji tsoro.”
Waɗansu Dokoki
22“Idan mutum ya yi laifin da ya isa mutuwa, aka rataye shi a itace har ya mutu, 23#Gal 3.13 kada a bar gawarsa ta kwana a kan itacen. Sai ku binne shi a ranar da aka rataye shi, gama wanda aka rataye shi la'ananne ne ga Ubangiji. Ku binne shi don kada ku ƙazantar da ƙasar da Ubangiji Allah yake ba ku, ku gāda.”
Currently Selected:
M.Sh 21: HAU
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979

: