YouVersion Logo
Search Icon

M.Sh 14

14
Al'adar Makokin da Aka Hana
1 # L.Fir 19.28; 21.5 “Ku 'ya'ya ne ga Ubangiji Allahnku, kada ku yi wa jikinku zāne, kada kuma ku yi wa kanku sanƙo saboda wani wanda ya rasu. 2#Fit 19.5,6; M.Sh 4.20; 7.6; 26.18; Tit 2.14; 1Bit 2.9 Gama ku keɓaɓɓun mutane ne na Ubangiji Allahnku. Ubangiji Allahnku kuwa ya zaɓo ku daga cikin dukan al'umman duniya ku zama mutanensa, wato abin gādonsa.”
Halattattun Dabbobi da Haramtattu
(L.Fir 11.1-47)
3“Kada ku ci abin da yake haram. 4Ga dabbobin da za ku ci, da saniya, da tunkiya, da akuya, 5da mariri, da barewa, da mariya, da mazo, da makwarna, da gada, da ɓauna, da ragon dutse. 6Za ku iya cin kowace dabbar da take da rababben kofato, wadda kuma take tuƙa. 7Amma duk da haka cikin waɗanda suke tuƙa, da waɗanda suke da rababben kofato ba za ku ci raƙumi, da zomo, da rema ba, ko da yake suna tuƙa, amma ba su da rababben kofato. Haram ne su a gare ku. 8Ba kuma za ku ci alade ba, ko da yake yana da rababben kofato, amma ba ya tuƙa. Haram ne shi a gare ku. Kada ku ci naman irin waɗannan dabbobi, ko ku taɓa mushensu.
9“Daga dukan irin abin da yake zaune a ruwa za ku iya cin duk abin da yake da ƙege da ɓamɓaroki. 10Kada ku ci duk irin abin da ba shi da ƙege ko ɓamɓaroki, gama haram yake a gare ku.
11“Kuna iya cin dukan halattattun tsuntsaye. 12Amma waɗannan tsuntsaye ne ba za ku ci ba, mikiya, da gaggafa, da ungulun kwakwa, 13da duki, da buga zabi, da kowace irin shirwa, 14da kowane irin hankaka, 15da jimina, da ƙururu, da bubuƙuwa, da kowane irin shaho, 16da mujiya, da babbar mujiya, da ɗuskwi, 17da kwasakwasa, da ungulu, da dimilmilo, 18da zalɓe, da kowane irin jinjimi, da katutu, da yaburbura.
19“Dukan 'yan ƙwari masu fikafikai masu rarrafe haram ne a gare ku, kada ku ci su. 20Za ku iya cin duk abin da yake da fikafikai in dai shi halattacce ne.
21 # Fit 23.19; 34.26 “Kada ku ci mushe. Amma mai yiwuwa ne ku ba baren da yake zaune a garuruwanku, ko kuma ku sayar wa baƙo. Gama ku jama'a ce keɓaɓɓiya ga Ubangiji Allahnku.
“Kada ku dafa ɗan akuya a madarar uwarsa.”
Dokar Zakar
22 # L.Fir 27.30-33; L.Ƙid 18.21 “Ku fitar da zakar dukan amfanin da kuka shuka a gonarku kowace shekara. 23Ku ci zakar sabon hatsinku, da ruwan inabinku, da manku, da 'yan fari na shanunku, da tumakinku, a gaban Ubangiji Allahnku, a wurin da zai zaɓa ya tabbatar da sunansa, don ku koyi tsoron Ubangiji Allahnku har abada. 24Idan ya zamana wurin ya yi muku nisa, har ba za ku iya kai zakar a wurin ba, saboda wurin da Ubangiji Allahnku ya zaɓa domin ya tabbatar da sunansa ya yi muku nisa sa'ad da Ubangiji Allahnku ya sa muku albarka, 25to, sai ku sayar da zakar, ku tafi da kuɗin wurin da Ubangiji Allahnku ya zaɓa, 26ku kashe kuɗin a kan duk abin da kuke so, ko sa ne, ko tunkiya, ko ruwan inabi, ko abin sha mai gafi, ko dai duk irin abin da ranku yake so. Nan za ku yi liyafa a gaban Ubangiji Allahnku, ku yi murna tare da iyalan gidanku.
27“Amma fa, kada ku manta da Balawen da yake garuruwanku gama ba shi da gādo kamarku. 28A ƙarshen kowace shekara uku, sai ku kawo dukan zakar abin da kuka girbe a wannan shekara, ku ajiye a ƙofofinku. 29Sa'an nan sai Balawe, da yake shi ba shi da gādo kamarku, da baƙo, da maraya, da gwauruwa ta gaske, waɗanda suke zaune a garuruwanku, su zo, su ci, su ƙoshi, domin Ubangiji Allahnku ya sa muku albarka cikin dukan aikin da hannunku zai yi.”

Currently Selected:

M.Sh 14: HAU

Highlight

Copy

Compare

Share

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in