Dan 8:19-21
Dan 8:19-21 HAU
Ya ce mini, “Zan sanar da kai abubuwan banhaushi, da za su faru nan gaba, gama wahayin ya shafi ƙayyadadden lokaci na ƙarshe. “Ragon nan mai ƙaho biyu da ka gani, sarakunan Mediya ne da na Farisa. Bunsurun kuwa Sarkin Hellas ne. Babban ƙahon nan da yake tsakanin idanunsa shi ne sarki na farko.



