Dan 5:25-28
Dan 5:25-28 HAU
Wannan shi ne rubutun da aka yi, MENE, MENE, TEKEL, da UPHARSIN. Ma'anar wannan ita ce, MENE, wato Allah ya sa kwanakin mulkinka su ƙare, sun kuwa ƙare. Ma'anar TEKEL ita ce an auna ka a ma'auni, aka tarar ka kāsa. Ma'anar PERES ita ce an raba mulkinka, an ba mutanen Mediya da na Farisa.”





