Kol 2:16-17
Kol 2:16-17 HAU
Saboda haka, kada ku damu in wani ya zarge ku a kan abin da kuke ci, ko abin da kuke sha, ko kuwa kan rashin kiyayewar wani idi, ko tsayawar wata, ko Asabar. Waɗannan kam, isharori ne kawai na abin da zai auku, amma Almasihu shi ne ainihinsu.





