YouVersion Logo
Search Icon

2Tas 2

2
Sarkin Tawaye
1 # 1Tas 4.15-17 To, a game da komowar Ubangijinmu Yesu Almasihu, da kuma taruwarmu mu sadu da shi, muna roƙonku 'yan'uwa, 2kada ku yi saurin jijiguwa a zukatanku, ko kuwa hankalinku yă tashi, saboda faɗar wani ruhu, ko wani jawabi, ko wata wasiƙa a kan cewa daga gare mu suke, cewa ranar Ubangiji ta zo.
3Kada ku yarda kowa yă yaudare ku ko ta halin ƙaƙa, domin wannan rana ba za ta zo ba, sai an yi fanɗarewar nan, sarkin tawaye kuma ya bayyana, wato, hallakakken nan. 4#Dan 11.36; Eze 28.2 Shi ne magabci, mai ɗaukaka kansa, yana gāba da duk abin da ya shafi sunan Allah, ko kuma wanda ake yi wa ibada. Har ma yakan zauna a Haikalin Allah, yana cewa, shi ne Allah. 5Ashe, ba ku tuna ba, nakan gaya muku haka tun muna tare? 6To, a yanzu dai kun san abin da yake tare shi, don kada ya bayyana kafin lokacinsa. 7Ko a yanzu ma tawayen nan, wanda ba shi fahimtuwa, an fara shi, amma farawar abin da zai faru, sai an ɗauke wanda yake hana shi tukuna. 8#Ish 11.4 A sa'an nan ne fa sarkin tawayen zai bayyana, Ubangiji Yesu kuwa zai hallaka shi da hucin bakinsa, ya kuma shafe shi da bayyanarsa a ranar komowarsa. 9#Mat 24.24 Mai tawayen nan kuwa, zai zo ne bisa ga ikon Shaiɗan, yana aikata abubuwan al'ajabi, da alamu, da aikin dabo na ƙarya iri iri, 10yana kuma yaudarar waɗanda suke a hanyar hallaka, muguwar yaudara, domin sun ƙi ƙaunar gaskiya har yadda za su sami ceto. 11Saboda haka, Allah zai auko musu da wata babbar ɓatan basira don su gaskata ƙarya, 12don duk a hukunta waɗanda suka ƙi gaskata gaskiya, suke kuma jin daɗin mugunta.
Ya Zaɓe Ku Ku Sami Ceto
13Ya ku 'yan'uwa, ƙaunatattun Ubangiji, lalle ne kullum mu gode wa Allah saboda ku, domin Allah ya zaɓe ku, don ku fara samun ceto ta wurin tsarkakewar Ruhu, da kuma amincewarku da gasikya. 14Domin wannan maƙasudi ya kira ku, ta wurin bishararmu, domin ku sami ɗaukakar Ubangijinmu Yesu Almasihu. 15Saboda haka, 'yan'uwa, sai ku dage, ku kuma riƙi ka'idodin da muka koya muku kankan, ko da baka ko ta wurin wasiƙa.
16To, Ubangijinmu Yesu Almasihu kansa, da kuma Allah Ubanmu, wanda ya ƙaunace mu, ya kuma ba mu madawwamiyar ta'aziyya da kyakkyawan bege ta wurin alherinsa, 17yă ta'azantar da ku, ya kuma ƙarfafa ku ga yin kowane kyakkyawan aiki da magana.

Currently Selected:

2Tas 2: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in

YouVersion uses cookies to personalize your experience. By using our website, you accept our use of cookies as described in our Privacy Policy