2Sam 23:3-4
2Sam 23:3-4 HAU
Allah na Isra'ila ya yi magana, Matsaron Isra'ila ya ce mini, ‘Sarkin da yake mulkin mutane da adalci, Wanda yake mulki da tsoron Allah, Yana kama da hasken rana a kan girgijen alfijir, Rana da take sa ciyawa ta yi ƙyalƙyali bayan an gama ruwan sama.’





