2Sam 22
22
Waƙar Nasarar Dawuda
(Zab 18)
1Wannan waƙa Dawuda ya raira wa Ubangiji sa'ad da Ubangiji ya cece shi daga hannun Saul da dukan sauran abokan gābansa, ya ce,
2“Ubangiji ne mai cetona,
Shi ne ƙaƙƙarfar kagarata.
3Allahna, shi ne kāriyata,
Ina zaune lafiya tare da shi.
Yana kāre ni kamar garkuwa,
Yana tsare ni, ya kiyaye ni.
Shi ne mai cetona.
4Na yi kira ga Ubangiji,
Ya cece ni daga abokan gābana.
Yabo ya tabbata ga Ubangiji!
5Gama raƙuman ruwa na mutuwa sun kewaye ni,
Raƙuman ruwa na hallaka suna gangarawa ta kaina.
6Mutuwa ta ɗaure ni da igiyoyinta da ƙarfi,
Kabari kuma ya ɗana mini tarko.
7A cikin wahalata na yi kira ga Ubangiji,
Na yi kira ga Allah domin taimako.
Daga cikin Haikalinsa ya ji muryata,
Ya kasa kunne ga kukana na neman taimako.
8“Sa'an nan duniya ta yi tangaɗi, ta girgiza,
Harsashin sararin sama ya yi makyarkyata, ya raurawa, saboda fushin Allah.
9Hayaƙi ya fito daga kafafen hancinsa,
Harshen wuta mai cinyewa da garwashi mai ƙuna daga bakinsa.
10Ya jā sararin sama baya ya sauko,
Da girgije mai duhu a ƙarƙashin ƙafafunsa.
11Ya hau kerub, ya tashi sama,
Ya yi tafiya ta fikafikan iska.
12Ya rufe kansa da duhu,
Gizagizai masu kauri cike da ruwa suna kewaye da shi,
13Garwashi mai ci daga tsawar walƙiya a gabansa.
14“Ubangiji ya yi tsawa daga sararin sama
Aka kuma ji muryar Maɗaukaki.
15Ya harharba kibau, ya warwatsa magabtansa,
Da walƙiyoyin tsawa ya sa su gudu.
16An bayyana ƙarƙashin teku a fili,
An tone tussan duniya,
Lokacin da Ubangiji ya yi wa abokan gāba tsautawa,
Ya yi musu ruri cikin fushi.
17Daga Sama Ubangiji ya miƙo ya ɗauke ni,
Ya tsamo ni daga zurfafan ruwaye.
18Ya kuɓutar da ni daga waɗanda suke ƙina,
Daga abokan gābana, waɗanda suka fi ƙarfina!
19Sa'ad da nake cikin wahala sun auka mini,
Amma Ubangiji ya kiyaye ni.
20Ya taimake ni ya fisshe ni daga hatsari,
Ya cece ni domin yana jin daɗina.
21“Ubangiji ya sāka mini bisa ga adalcina,
Ya sa mini albarka domin ba ni da laifin kome.
22Gama na kiyaye dokar Ubangiji,
Ban yi wa Allahna tayarwa ba.
23Na kiyaye dukan dokokinsa,
Ban yi rashin biyayya ga umarnansa ba.
24Ya sani ni marar laifi ne,
Na kiyaye kaina daga aikata mugunta.
25Domin haka ya sāka mini bisa ga adalcina,
Gama ya sani ba ni da laifi.
26“Kai, ya Ubangiji, amintacce ne ga waɗanda suke da aminci,
Nagari ne kuma ga waɗanda suke cikakku.
27Mai Tsarki ne kai ga waɗanda suke tsarkaka,
Amma kana gāba da waɗanda suke mugaye.
28Kakan ceci masu tawali'u,
Amma kakan ƙasƙantar da masu girmankai.
29“Ya Ubangiji, kai ne haskena,
Kana haskaka duhuna.
30Ka ba ni ƙarfi don in auka wa abokan gābana,
Da iko domin in murƙushe tsaronsu.
31“Allahn nan cikakke ne ƙwarai,
Maganarsa tabbatacciya ce!
Kamar garkuwa yake
Ga dukan masu neman kiyayewarsa.
32Ubangiji shi kaɗai ne Allah,
Allah ne kaɗai madogararmu.
33Allahn nan shi ne mafaka, mai ƙarfi ne a gare ni,
Ya sa hanyata ta zama lafiyayyiya.
34 #
Hab 3.19
Ya mai da ƙafafuna kamar na barewa,
Ya kiyaye ni a kan duwatsu.
35Ya horar da ni domin yaƙi,
Domin in iya tausa baka mafi ƙarfi.
36“Ya Ubangiji, ka kiyaye ni, ka cece ni,
Taimakonka ya sa na zama babba.
37Ka hana a kama ni,
Ban kuwa taɓa faɗuwa ba.
38Na runtumi abokan gābana, na kuwa hallaka su,
Ban tsaya ba sai da na kore su.
39Na fyaɗa su ƙasa, ba su iya tashi ba,
Suna kwance warwar a ƙafafuna.
40Ka ba ni ƙarfi domin yin yaƙi,
Nasara kuma a kan abokan gābana.
41Ka sa abokan gābana su gudu daga gabana,
Na hallaka waɗanda suke ƙina.
42Suka nemi taimako, amma ba wanda zai cece su,
Suka yi kira ga Ubangiji, amma bai amsa musu ba.
43Na murƙushe su, sun yi laushi kamar ƙura,
Na tattake su kamar caɓi a kan tituna, na kuwa watsar da su.
44“Ka cece ni daga jama'ata mai tawaye,
Ka sa in yi mulkin al'ummai,
Mutanen da ban san su ba sun zama bayina.
45Baƙi sun zo suna rusuna mini,
Sa'ad da suka ji ni suka yi mini biyayya.
46Zuciyarsu ta karai,
Suka fito daga kagararsu suna rawar jiki.
47“Ubangiji mai rai ne! Yabo ya tabbata ga mai tsaronsa!
Allah ne ƙaƙƙarfan Mai Cetona! Ku yi shelar girmansa!
48Ya ba ni nasara a kan abokan gabana,
Ya sa mutane a ƙarƙashin mulkina,
49Ya kuɓutar da ni daga hannun maƙiya.
Kai, ya Ubangiji, ka ba ni nasara a kan maƙiyana,
Ka tsare ni daga mutane masu zafin hali.
50 #
Rom 15.9
Domin wannan zan yi yabonka cikin al'ummai,
Zan raira yabbai gare ka.
51Allah ya ba sarkinsa manya manyan nasarori,
Ya nuna madawwamiyar ƙauna ga shi wanda ya zaɓa,
Wato ga Dawuda da zuriyarsa har abada.”
Currently Selected:
2Sam 22: HAU
Highlight
Share
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979

:
Highlight
Share
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979