YouVersion Logo
Search Icon

2Sam 11

11
Dawuda da Bat-Sheba
1 # 1Tar 20.1 Da bazara lokacin da sarakuna sukan fita zuwa yaƙi, Dawuda ya aiki Yowab, da shugabannin sojojinsa, da sojojin Isra'ila duka. Suka tafi suka ragargaza Ammonawa, suka kuma kewaya Rabba da yaƙi. Amma Dawuda ya yi zamansa a Urushalima.
2Wata rana da yamma Dawuda ya tashi daga shaƙatawa, yana yawo a kan rufin soron fādarsa, can ya hangi wata kyakkyawar mata tana wanka. 3Sai ya aika a bincika ko wace ce wannan mata, ashe, 'yar Ammiyel ce, matar Uriya Bahitte. 4Dawuda kuwa ya aiki waɗansu manzanni suka kawo masa ita, ya kwana da ita. (A lokacin kuwa ta gama wankan haila ke nan.) Sa'an nan ta koma gidanta. 5Matar kuwa ta yi juna biyu, sai ta aika a faɗa wa Dawuda, cewa, tana da ciki.
6Dawuda kuwa ya aika wurin Yowab ya ce, “Ka aiko mini da Uriya Bahitte.” Yowab kuwa ya aika da Uriya wurin Dawuda. 7Da Uriya ya iso, sai Dawuda ya tambaye shi labarin Yowab, da lafiyar jama'ar, da labarin yaƙin. 8Ya kuma ce masa, “Ka tafi gidanka, ka wanke ƙafafunka.” Da Uriya ya fita daga gidan sarki, sarki ya ba da kyauta a kai masa. 9Amma Uriya bai tafi gidansa ba, sai ya kwana a ƙofar gidan sarki tare da sauran barorin sarki. 10Da aka faɗa wa Dawuda, cewa, Uriya bai tafi gidansa ba, Dawuda ya kira Uriya ya ce masa, “Ka dawo daga tafiya, me ya sa ba ka tafi gidanka ba?”
11Uriya ya ce wa Dawuda, “Akwatin alkawari, da mutanen Isra'ila, da na Yahuza, suna zaune a bukkoki. Shuganana Yowab, da barorinsa suna zaune a sansani a karkara, ƙaƙa ni zan tafi gidana in ci in sha, in kwanta da matata? Na rantse da ranka, ba zan yi haka ba.”
12Dawuda kuma ya ce wa Uriya, “Ka kwana nan kuma yau, gobe in sallame ka.” Sai Uriya ya kwana a Urushalima a ran nan. 13Kashegari kuma Dawuda ya kira shi liyafa. Ya zo, ya ci ya sha tare da shi, har Dawuda ya sa shi ya bugu. Amma da dare, sai ya tafi ya kwanta a shimfiɗarsa tare da sauran barorin sarki, amma bai tafi gidansa ba.
14Da safe Dawuda ya rubuta wasiƙa, ya ba Uriya ya kai wa Yowab. 15A wasiƙar ya ce wa Yowab, “Tura Uriya a gaba a inda yaƙin ya fi zafi, sa'an nan ku ja da baya, ku bar shi don a buge shi a kashe shi.” 16Sa'ad da Yowab yake kama garin da yaƙi, sai ya sa Uriya a inda ya sani akwai jarumawan gaske. 17Mutanen garin suka fito suka yi yaƙi da Yowab. Suka kashe waɗansu daga cikin sojojin Dawuda. Uriya Bahitte, shi ma aka kashe shi.
18Sai Yowab ya aika aka faɗa wa Dawuda labarin yaƙin. 19-20Ya ce wa manzo, “Bayan da ka gama faɗa wa sarki labarin yaƙin duka, idan sarki ya husata, har ya ce maka, ‘Me ya sa kuka tafi yaƙi kurkusa da garin? Ba ku sani ba za su tsaya a gefen garu daga ciki su yi harbi? 21#L.Mah 9.53 Wa ya kashe Abimelek ɗan Yerubba'al? Ba mace ce a Tebeze ta jefe shi da ɗan dutsen niƙa ta kan garu daga ciki ta kashe shi ba? Me ya sa kuka tafi kusa da garu?’ Sai ka faɗa masa cewa, ‘Baranka, Uriya Bahitte, shi ma an kashe shi.’ ”
22Manzon kuwa ya tafi ya faɗa wa Dawuda dukan abin da Yowab ya ce. 23Ya ce, “Abokan gābanmu sun sami sa'a a kanmu. Sun fito su gabza da mu a karkara, amma muka kore su zuwa cikin ƙofar garin. 24Sai maharba suka tsaya a kan garu daga ciki suka yi ta harbin barorinka. Waɗansu daga cikin barorin sarki sun mutu. Baranka Uriya Bahitte shi ma ya matu.”
25Dawuda ya ce wa manzon, “Je ka ka faɗa wa Yowab kada wannan abu ya dame shi, ai, takobi ba ya tarar wanda zai kashe. Ku ƙara matsa wa garin lamba, ku faɗa masa har ku ragargaza shi. Ka ƙarfafa Yowab.”
26Sa'ad da matar Uriya ta ji labarin mutuwar mijinta, ta yi makoki dominsa. 27Da kwanakin makokin suka ƙare, sai Dawuda ya aika aka kawo ta gidansa, ta zama matarsa, ta haifa masa ɗa. Amma Ubangiji bai ji daɗin mugun abin nan da Dawuda ya yi ba.

Currently Selected:

2Sam 11: HAU

Highlight

Share

Compare

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in