YouVersion Logo
Search Icon

1Tas 5

5
Ku Zauna a Faɗake don Zuwan Ubangiji
1Amma ga zancen ainihin lokaci ko rana, ba lalle sai an rubuto muku kome ba. 2#Mat 24.43; Luk 12.39; 2Bit 3.10 Domin ku da kanku kun sani sarai, ranar Ubangiji za ta zo ne kamar ɓarawo da dare. 3Lokacin da mutane suke cewa, “Muna zaman salama da zaman lafiya,” wuf; sai halaka ta auko musu, kamar yadda naƙuda take kama mace mai ciki, ba kuwa hanyar tsira. 4Amma, ai, ba a cikin duhu kuke ba, 'yan'uwa, har da ranar nan za ta mamaye ku kamar ɓarawo. 5Domin duk mutanen haske kuke, na rana kuma. Mu ba na dare ko na duhu ba ne. 6Ashe, saboda haka kada mu yi barci yadda waɗansu suke yi, sai dai mu zauna a faɗake, da natsuwa. 7Don masu barci da daddare suke barci, masu sha su bugu ma da daddare suke sha su bugu. 8#Ish 59.17; Afi 6.13-17 Amma da yake mu na rana ne, sai mu natsu, muna saye da sulken bangaskiya da ƙauna, muna begen samun ceto, shi ne kuma kwalkwakinmu. 9Allah bai ƙaddara mu ga fushinsa ba, sai dai ga samun ceto ta wurin Ubangijinmu Yesu Almasihu, 10wanda ya mutu saboda mu, domin ko muna a raye, ko muna barci, mu zama muna tare da shi. 11Saboda haka, sai ku ƙarfafa wa juna zuciya, kuna riƙa inganta juna, kamar dai yadda kuke yi.
Gargaɗi da kuma Gaisuwa
12Amma muna roƙonku 'yan'uwa, ku girmama masu fama da aiki a cikinku, wato waɗanda suke shugabanninku cikin Ubangiji, suke kuma yi muku gargaɗi. 13Ku riƙe su da mutunci ƙwarai game da ƙauna saboda aikinsu. Ku yi zaman lafiya da juna. 14Muna kuma yi muku gargaɗi, 'yan'uwa, ku tsawata wa malalata, ku ƙarfafa masu rarraunar zuciya, ku taimaki marasa tsayayyiyar zuciya, ku yi haƙuri da kowa da kowa. 15Ku lura fa, kada kowa ya rama mugunta da mugunta. Sai dai kullum ku nace yi wa juna aiki nagari, da kuma dukkan mutane. 16Ku riƙa yin farin ciki a kullum. 17Ku riƙa yin addu'a ba fāsawa. 18Ku godiya ga Allah a kowane hali, domin shi ne nufin Allah a game da ku ta wurin Almasihu Yesu. 19Kada ku danne maganar Ruhu. 20Kada ku raina annabci, 21sai dai ku jarraba kome, ku riƙi abin da yake nagari kankan. 22Ku yi nesa da kowace irin mugunta.
23Allah kansa, mai zartar da salama, yă tsarkake ku sarai, ya kuma kiyaye ruhunku da ranku da jikinku ƙalau, ku kasance marasa abin zargi a ranar komowar Ubangijinmu Yesu Almasihu. 24Wanda yake kiranku ɗin nan mai alkawari ne, zai kuwa zartar.
25Ya ku 'yan'uwa, ku yi mana addu'a.
26Ku gai da dukkan 'yan'uwa da tsattsarkar sumba.
27Na gama ku da Ubangiji, a karanta wa dukkan 'yan'uwa wasiƙar nan.
28Alherin Ubangijinmu Yesu Almasihu yă tabbata a gare ku.

Currently Selected:

1Tas 5: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in

YouVersion uses cookies to personalize your experience. By using our website, you accept our use of cookies as described in our Privacy Policy