YouVersion Logo
Search Icon

1Kor 9

9
Hakkokin Manzo
1Ni ba ɗa ba ne? Ba kuma manzo ba ne? Ban ga Yesu Ubangijinmu ba ne? Ku ba aikina ba ne a cikin Ubangiji? 2Ai, ko waɗansu ba su ɗauke ni a kan manzo ba, lalle ku kam, ni manzo ne a gare ku, domin kuwa ku ne tabbatar manzancina a gaban Ubangiji.
3Wannan ita ce kariyata ga masu son tuhumata. 4Ashe, ba mu da iko a ba mu ci da sha? 5Ba mu da ikon tafiya da matarmu ta aure mai bi, kamar yadda sauran manzanni, da 'yan'uwan Ubangiji, da kuma Kefas suke yi? 6Ko kuwa dai ni da Barnaba ne kawai, ba mu da iko a ɗauke mana aikin ci da kai? 7Wa yake yin aikin soja, sa'an nan yă ci da kansa? Wa zai shuka garkar inabi, yă kasa cin 'ya'yan? Wa zai yi kiwon garke, yă kasa shan nonon?
8Wato, ina faɗar haka bisa ga ra'ayin mutum kawai ne? Ba haka ma Attaura ta faɗa ba? 9#M.Sh 25.4; 1Tim 5.18 Ai, haka yake a rubuce a Shari'ar Musa cewa, “Kada ka sa wa takarkari takunkumi a sa'ad da yake sussuka.” Da shanu ne kawai Allah yake kula? 10Ba saboda mu musamman yake magana ba? Hakika saboda mu ne aka rubuta. Ai, ya kamata mai noma yă yi noma da sa zuciya, mai sussuka kuma yă yi sussuka da sa zuciya ga samun rabo daga amfanin gonar. 11#Rom 15.27 Da yake mun shuka iri na ruhu a zuciyarku, to, wani ƙasaitaccen abu ne, in mun mori amfaninku irin na duniya? 12Da yake waɗansu sun mori halaliyarsu a game da ku, ashe ba mu muka fi cancanta ba?
Duk da haka ba mu mori wannan halaliya ba, sai dai muna jure wa kome, don ta koƙaƙa kada mu hana bisharar Almasihu yaɗuwa. 13#M.Sh 18.1 Ashe, ba ku sani ba, masu hidima a Haikali daga nan suke samun abincinsu? Masu hidimar bagadi kuma, a nan suke samun rabo daga hadayar da aka yanka? 14#Mat 10.10; Luk 10.7 Haka nan kuma Ubangiji ya yi umarni, cewa, ya kamata masu sanar da bishara, a cishe su albarkacin bishara.
15Amma ni kam, ban mori ko ɗaya daga cikin halaliyan nan ba, ba kuma ina rubuta wannan ne, don a yi mini haka ba. Ai, gara in mutu a kan wani ya banzanta mini fahariyata. 16Don ko da yake ina yin bishara, ba na fahariya da haka, gama tilas ne a gare ni. Kaitona in ba na yin bishara! 17Da da ra'ina nake yi, da sai a biya ni. Amma da yake ba da ra'ina ba ne, an danƙa mini amana ke nan. 18Ina kuma hakkina? To, ga shi. A duk lokacin da nake yin bishara, sona in yi ta a kyauta, kada in ƙurashe halaliyata a game da bishara.
19Ko da yake ni ba bawan kowa ba ne, na mai da kaina bawan kowa, domin in rinjayi mutane masu yawa. 20Ga Yahudawa, sai na zama kamar Bayahude, domin in rinjayi Yahudawa. Ga waɗanda Shari'a take iko da su, sai na zama kamar wanda Shari'a take iko da shi, ko da yake ba Shari'a take iko da ni ba, domin in rinjayi waɗanda Shari'a take iko da su ne. 21Ga marasa Shari'a kuwa, sai na zama kamar marar Shari'a, ba cewa ba wata shari'ar Allah da take iko da ni ba, a'a, shari'ar Almasihu na iko da ni, domin in rinjayi marasa Shari'a ne. 22Ga raunana, sai na zama kamar rarrauna domin in rinjayi raunana. Na zama kowane irin abu ga ko waɗanne irin mutane, domin ta ko ƙaƙa in ceci waɗansu. 23Na yi wannan ne duk saboda bishara, domin in sami rabo a cikin albarkarta.
24Ashe, ba ku sani ba, a wajen tsere dukan masu gudu suna ƙoƙarin tsere wa juna, amma ɗaya ne kaɗai yake samun kyautar ci? To, sai ku yi ta gudu haka nan, don ku ci. 25Duk masu wasan gasa, sukan hori kansu ta kowane hali. Su kam, suna yin haka ne, don su sami lada mai lalacewa, mu kuwa marar lalacewa. 26To, ni ba gudu nake yi ba wurin zuwa ba, dambena kuwa ba naushin iska nake yi ba. 27Amma ina azabta jikina ne, don in bautar da shi, kada bayan da na yi wa waɗansu wa'azi, ni da kaina a yar da ni.

Currently Selected:

1Kor 9: HAU

Highlight

Copy

Compare

Share

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in