Filibbiyawa 3:13-14
Filibbiyawa 3:13-14 SRK
’Yan’uwa, ban ɗauki kaina a kan cewa na riga na sami abin ba. Sai dai abu guda nake yi. Ina mantawa da abin da yake baya, ina kuma nacewa zuwa ga samun abin da yake gaba, ina nacewa gaba zuwa ga manufar, don in sami ladar da Allah ya yi mini na kiran nan zuwa sama a cikin Kiristi Yesu.