YouVersion Logo
Search Icon

Filibbiyawa 2:1-3

Filibbiyawa 2:1-3 SRK

In kuna da wata ƙarfafawa daga tarayya da Kiristi, in da wata ta’aziyya daga ƙaunarsa, in da wani zumunci da Ruhu, in da juyayi da tausayi, to, sai ku sa farin cikina yă zama cikakke ta wurin kasance da hali ɗaya, kuna ƙauna ɗaya, kuna zama ɗaya cikin ruhu da kuma manufa. Kada ku yi kome da sonkai ko girman kai, sai dai cikin tawali’u, ku ɗauki waɗansu sun fi ku.