Mattiyu 22:37-39
Mattiyu 22:37-39 SRK
Yesu ya amsa ya ce, “ ‘Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka da dukan ranka da kuma dukan hankalinka.’ Wannan, ita ce doka ta fari da kuma mafi girma. Ta biye kuma kamar ta farkon take. ‘Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.’











