YouVersion Logo
Search Icon

Kolossiyawa Gabatarwa

Gabatarwa
Gabatarwa
An rubuta wannan wasiƙa zuwa ga al’ummar Kirista a Kolossi, wani ƙaramin birni a Asiya Ƙarama wanda daga baya girgizar ƙasa ta rushe a shekara ta 60 bhy Ba Bulus ne ya kafa ikkilisiya a Kolossi ba, Efafaras ne, wani Kirista wanda yake shugaba, wanda sau da dama aka ambata a cikin wasiƙar, wanda ya kasance a kurkuku tare da Bulus a lokacin da aka rubuta wasiƙan nan. Wasiƙar ta gargaɗe Kirista waɗanda su Kolossiyawa ne, da su guji koyarwar ƙaryar da ta ɗauka cewa sani yana da muhimmanci fiye da bangaskiya, su guji bin addinin da ya haɗa da yin wa mala’iku sujada, su kuma guji kamunkan da ya wuce gona da iri. Wasiƙar ta tuna wa masu karatu cewa Kiristi shi ne maƙasudin asirin Allah, ta kuma bayyana abin da ake nufin da a tā da mutum da rai tare da Kiristi. Wasiƙar ta ƙarfafa Kolossiyawa su bar saƙon Yesu yă mamaye rayuwarsu, ta kuma jera dokoki don rayuwar Kirista.

Currently Selected:

Kolossiyawa Gabatarwa: SRK

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in