Ayyukan Manzanni 7:8
Ayyukan Manzanni 7:8 SRK
Sa’an nan ya yi wa Ibrahim alkawari game da kaciya. Ibrahim kuwa ya zama mahaifin Ishaku ya kuma yi masa kaciya kwana takwas bayan haihuwarsa. Daga baya Ishaku ya zama mahaifin Yaƙub, Yaƙub kuma ya zama mahaifin kakanninmu sha biyun nan.





