Ayyukan Manzanni 7:57-58
Ayyukan Manzanni 7:57-58 SRK
Da jin haka sai suka tattoshe kunnuwansu, suka kuma yi ihu da ƙarfi sosai, suka aukar masa gaba ɗaya. Suka ja shi zuwa bayan birnin suka kuma yi ta jifansa da duwatsu. Ana cikin haka, shaidun suka ajiye tufafinsu a wurin wani saurayi mai suna Shawulu.





