Ayyukan Manzanni 3:7-8
Ayyukan Manzanni 3:7-8 SRK
Ta wurin kama hannunsa na dama, ya taimake shi ya miƙe, nan take ƙafafu da idon sawun mutumin suka yi ƙarfi. Sai ya yi wuf da ƙafafunsa ya fara tafiya. Ya tafi tare da su ya shiga cikin filin haikali yana tafiya yana tsalle, yana kuma yabon Allah.





