Ayyukan Manzanni 28:26-27
Ayyukan Manzanni 28:26-27 SRK
“ ‘Je ka wurin mutanen nan ka ce, “Za ku yi ta ji amma ba za ku fahimta ba; za ku yi ta dubawa, amma ba za ku gani ba.” Gama zuciyar mutanen nan ta yi tauri; da ƙyar suke ji da kunnuwansu, sun kuma rufe idanunsu. In ba haka ba za su iya gani da idanunsu, su ji da kunnuwansu, su fahimta a zukatansu, su kuma juyo, in kuwa warkar da su.’





