1
Neh 7:1-2
Littafi Mai Tsarki
HAU
Sa'ad da aka gina garun, aka sa ƙofofinsa, aka kuma sa matsaran ƙofofi, da mawaƙa, da Lawiyawa, sai na ba ɗan'uwana, Hanani, da Hananiya, shugaban kagara, aikin riƙon Urushalima. Shi Hananiya mai aminci ne, mai tsoron Allah, fiye da sauran mutane.
Compare
Explore Neh 7:1-2
2
Neh 7:3
Sa'an nan na ce musu, kada su buɗe ƙofofin Urushalima da sassafe, sai rana ta cira sosai, su kuma kulle ƙofofin da ƙarfe kafin matsara su tashi wajen faɗuwar rana. Su samo matsara daga mazaunan Urushalima, su sa su tsaye a muhimman wurare, waɗansunsu kuma suna zaga gidaje.
Explore Neh 7:3