A wannan rana aka karanta daga littafin Musa a kunnuwan jama'a. A cikinsa aka tarar da inda aka rubuta, cewa kada Ba'ammone, ko mutumin Mowab ya shiga taron jama'ar Allah. Gama ba su taryi jama'ar Isra'ila da abinci da abin sha ba, amma suka yi ijara da Bal'amu ya zo ya la'anta musu su, amma Allahnmu ya juyar da la'anar ta zama albarka.