Na ce, “Ya Ubangiji Allah na Sama, Allah mai girma, mai banrazana, mai cika alkawari, mai nuna madawwamiyar ƙauna ga waɗanda suke ƙaunarka, wato masu kiyaye umarnanka, ina roƙonka ka kasa kunne, ka kuma buɗe idanunka, ka ji addu'ar bawanka, wadda nake yi a gabanka dare da rana saboda bayinka, mutanen Isra'ila. Ina hurta zunubanmu, mu mutanen Isra'ila, da muka yi maka. Ni da gidan ubana mun yi zunubi.