1
Josh 14:11
Littafi Mai Tsarki
HAU
Ga shi kuwa, har wa yau ina da ƙarfi kamar ran da Musa ya aike ni. Kamar yadda ƙarfina yake a dā, haka yake a yanzu domin yaƙi, da kuma kai da kawowa.
Compare
Explore Josh 14:11
2
Josh 14:12
Saboda haka sai ka ba ni ƙasar tuddai da Ubangiji ya ambata a ranan nan, gama a wannan rana ka ji yadda gwarzaye suke a can da manyan birane masu garu, mai yiwuwa ne Ubangiji zai kasance tare da ni, in kore su kamar yadda Ubangiji ya faɗa.”
Explore Josh 14:12
3
Josh 14:10
Ga shi kuwa, Ubangiji ya kiyaye ni har wa yau, kamar yadda ya faɗa, shekara arba'in da biyar ke nan, tun lokacin da Ubangiji ya faɗa wa Musa wannan magana, a lokacin da Isra'ilawa suke yawo a jeji. Ga shi yau ni mai shekara tamanin da biyar ne.
Explore Josh 14:10