1
Josh 10:13
Littafi Mai Tsarki
HAU
Sai rana ta tsaya cik, wata kuma ya tsaya, Har al'ummar ta ɗauki fansa a kan abokan gābansu. Ai, wannan a rubuce yake a littafin Yashar. Rana dai ta tsaya a tsaka, ta yi jinkirin faɗuwa da misalin yini guda.
Compare
Explore Josh 10:13
2
Josh 10:12
Sa'an nan Joshuwa ya yi magana da Ubangiji a gaban Isra'ilawa a ranar da Ubangiji ya ba da Amoriyawa gare su, ya ce, “Ke rana, ki tsaya a Gibeyon, Kai kuma wata, ka tsaya a kan kwarin Ayalon.”
Explore Josh 10:12
3
Josh 10:14
Ba a taɓa yin yini kamar wannan ba, ko kafin wannan yini, ko bayansa kuma, da Ubangiji ya saurari muryar mutum. Gama Ubangiji ya yi yaƙi domin Isra'ilawa.
Explore Josh 10:14
4
Josh 10:8
Ubangiji kuwa ya ce wa Joshuwa, “Kada ka ji tsoronsu gama na riga na ba da su a hannunka, ba mutuminsu da zai iya tsayawa a gabanka.”
Explore Josh 10:8
5
Josh 10:25
Sai Joshuwa ya ce musu, “Kada ku ji tsoro, ko kuwa ku razana, amma ku ƙarfafa, ku yi ƙarfin hali, gama haka Ubangiji zai yi da dukan abokan gābanku waɗanda za ku yi yaƙi da su.”
Explore Josh 10:25