Allah, da ikonsa, yakan hallaka masu ƙarfi,
Allah yakan aikata, sai mugun mutum ya mutu.
Ya yiwu Allah ya bar shi ya yi zamansa lafiya,
Amma a kowane lokaci zai sa ido a kansa.
Mugun mutum yakan ci nasara ɗan lokaci,
Daga nan sai ya yi yaushi kamar tsiro,
Ya yi yaushi kamar karan dawa da aka yanke.