Ubangiji ya ce,
“Ya mutanen Isra'ila, idan za ku
juyo ku komo wurina,
Idan kuka kawar da abubuwan
banƙyama daga gabana,
Kuka kuma bar yin shakka,
Idan kun yi rantsuwa kuka ce,
‘Har da ran Ubangiji kuwa,’
Da gaskiya, da aminci, da adalci,
Sa'an nan sauran al'umma za su so
in sa musu albarka,
Za su kuma yabe ni.”