1
Yak 1:2-3
Littafi Mai Tsarki
HAU
Ya ku 'yan'uwana, duk sa'ad da gwaje-gwaje iri iri suka same ku, ku mai da su abin farin ciki ƙwarai. Domin kun san jarrabawar bangaskiyarku takan haifi jimiri.
Compare
Explore Yak 1:2-3
2
Yak 1:5
In waninku ya rasa hikima, sai ya roƙi Allah, mai ba kowa hannu sake, ba tare da gori ba, sai kuwa a ba shi.
Explore Yak 1:5
3
Yak 1:19
Ya 'yan'uwana ƙaunatattu, ku san wannan, wato, kowa yă yi hanzarin kasa kunne, da jinkirin yin magana, da kuma jinkirin yin fushi
Explore Yak 1:19
4
Yak 1:4
Sai kuma jimiri ya yi cikakken aikinsa, domin ku zama kamilai cikakku kuma, ba ku gaza da kome ba.
Explore Yak 1:4
5
Yak 1:22
Amma ku zama masu aikata maganar, ba masu ji kawai, kuna yaudarar kanku ba.
Explore Yak 1:22
6
Yak 1:12
Albarka tā tabbata ga mai jimirin gwaji, domin in ya jure gwajin, sai ya sami kambin rai, wanda Ubangiji ya yi wa masu ƙaunarsa alkawari.
Explore Yak 1:12
7
Yak 1:17
Kowace kyakkyawar baiwa, da kowace cikakkiyar kyauta, daga Sama suke, sun sauko ne daga wurin Uban haskoki, wanda ba sauyawa ko wata alamar sākewa a gare shi faufau.
Explore Yak 1:17
8
Yak 1:23-24
Don duk wanda yake mai jin maganar ne kawai, ba mai aikatawa ba, kamar mutum yake mai duba fuskarsa a madubi, don yakan dubi fuskarsa ne kawai ya tafi, nan da nan kuwa sai ya mance kamanninsa.
Explore Yak 1:23-24
9
Yak 1:27
Addini sahihi kuma marar aibu a gaban Allah Ubanmu, shi ne a kula da gwauraye mata, da marayu a cikin ƙuntatarsu, a kuma a keɓe kai marar aibi daga duniya.
Explore Yak 1:27
10
Yak 1:13-14
Duk wanda ake jarabta, kada ya ce Allah ne yake jarabtarsa, gama ba shi yiwuwa a jarabci Allah da mugunta, shi kansa kuwa ba ya jarabtar kowa. Amma kowane mutum yakan jarabtu in mugun burinsa ya ruɗe shi, ya kuma yaudare shi.
Explore Yak 1:13-14
11
Yak 1:9
Ƙasƙantaccen ɗan'uwa yă yi taƙama da ɗaukakarsa.
Explore Yak 1:9
Home
Bible
Plans
Videos