Sarautar ikonsa za ta yi ta ci gaba,
Mulkinsa zai kasance da salama kullayaumin,
Zai gāji sarki Dawuda, ya yi mulki a matsayinsa,
Zai kafa mulkinsa a kan adalci da gaskiya,
Tun daga yanzu har zuwa ƙarshen zamani.
Ubangiji Mai Runduna ne ya yi niyyar aikata wannan duka.