1
Ish 60:1
Littafi Mai Tsarki
HAU
Ki tashi, ya Urushalima, ki haskaka kamar rana, Daukakar Ubangiji tana haskakawa a kanki kamar rana!
Compare
Explore Ish 60:1
2
Ish 60:3
Za a jawo al'ummai zuwa ga haskenki, Sarakuna kuma zuwa asubahin sabon yininki.
Explore Ish 60:3
3
Ish 60:2
Duhu zai rufe sauran al'umma, Amma hasken Ubangiji zai haskaka a kanki, Daukakarsa za ta kasance tare da ke!
Explore Ish 60:2
4
Ish 60:22
Har ma da iyalin da suka fi ƙanƙanta da ƙasƙanci, Za su zama babbar al'umma, Kamar al'umma mai iko. Zan sa wannan ya faru nan da nan Sa'ad da lokacin da ya dace ya yi. Ni ne Ubangiji!”
Explore Ish 60:22
5
Ish 60:19
“Rana ba za ta ƙara zama haskenki da rana ba, Ko wata ya zama haskenki da dare. Ni, Ubangiji, zan zama madawwamin haskenki, Hasken ɗaukakata zai haskaka a kanki.
Explore Ish 60:19
6
Ish 60:20
Kwanakin baƙin cikinki za su ƙare. Ni, Ubangiji, zan zama madawwamin haskenki, Mai daɗewa fiye da na rana da na wata.
Explore Ish 60:20
7
Ish 60:5
Za ki ga wannan, ki cika da farin ciki, Za ki yi rawar jiki saboda jin daɗi. Za a kawo miki dukiyar al'ummai, Wato waɗanda suke a ƙasashen hayi.
Explore Ish 60:5
8
Ish 60:4
Ki duba kewaye da ke, ki ga abin da yake faruwa, Mutanenki suna ta tattaruwa domin su komo gida! 'Ya'yanki maza za su taho daga nesa, Za a ɗauki 'ya'yanki mata kamar yara.
Explore Ish 60:4
9
Ish 60:21
Dukan mutanenki za su yi abin da yake daidai, Za su kuwa mallaki ƙasar har abada. Ni na dasa su, ni na yi su Domin su bayyana girmana ga duka.
Explore Ish 60:21
10
Ish 60:18
Ba za a ƙara jin hayaniyar tashin hankali ba, Ba za a ƙara aukar wa ƙasar da ɓarna ba. Zan kiyaye ki, in kāre ki kamar garu, Za ki yi yabona domin na cece ki.
Explore Ish 60:18
11
Ish 60:11
Ƙofofinki za su kasance a buɗe dare da rana, Domin sarakunan al'ummai su kawo miki dukiyarsu.
Explore Ish 60:11
12
Ish 60:6
Babban ayarin raƙuma zai zo daga Madayana da Efa. Za su zo daga Sheba, su kawo zinariya da kayan ƙanshi. Mutane za su ba da labari mai daɗi a kan abin da Allah ya yi!
Explore Ish 60:6
13
Ish 60:10
Ubangiji ya ce wa Urushalima, “Baƙi ne za su sāke gina garukanki, Sarakunansu kuma za su bauta miki. Na hukunta ki da fushina, Amma yanzu zan nuna miki alheri da jinƙai.
Explore Ish 60:10
14
Ish 60:15
“Ba za a ƙara ƙinki, a yashe ki ba, Ki zama birnin da aka fita aka bari ba kowa ciki. Zan sa ki zama babba, mai ƙayatarwa kuma, Wurin yin farin ciki har abada abadin.
Explore Ish 60:15
15
Ish 60:16
Al'ummai da sarakuna za su lura da ke Kamar yadda uwa take lura da ɗanta. Za ki sani, ni Ubangiji, na cece ki, Allah Mai Iko Dukka na Isra'ila ya fanshe ki.
Explore Ish 60:16
Home
Bible
Plans
Videos