1
Ish 6:8
Littafi Mai Tsarki
HAU
Sai na ji Ubangiji yana cewa, “Wa zan aika? Wa zai zama manzonmu?” Sai na amsa na ce, “Ga ni! Ka aike ni!”
Compare
Explore Ish 6:8
2
Ish 6:3
Suna ta kiran junansu suna cewa, “Mai Tsarki, Mai Tsarki, Mai Tsarki! Ubangiji Mai Runduna Mai Tsarki ne! Ɗaukakarsa ta cika duniya.”
Explore Ish 6:3
3
Ish 6:5
Sai na ce, “Sa zuciyata ya ƙare! Na shiga uku! Kowace maganar da ta fito bakina zunubi ce, ina zaune a tsakanin mutane waɗanda duk maganarsu zunubi ce, ba ta da tsarki. Amma yanzu da idona na ga Sarki, Ubangiji Mai Runduna!”
Explore Ish 6:5
4
Ish 6:1
A shekarar da sarki Azariya ya rasu na ga Ubangiji. Yana zaune a kursiyinsa a Sama cike da ɗaukaka, zatinsa ya cika Haikali.
Explore Ish 6:1
5
Ish 6:7
Ya taɓa leɓunana da garwashin wutar ya ce, “Wannan ya taɓa leɓunanka, yanzu fa an kawar da laifofinka, an kuma gafarta maka zunubanka.”
Explore Ish 6:7
6
Ish 6:2
Kewaye da shi sai ga waɗansu talikai masu kama da harshen wuta a tsaye, ko wannensu yana da fikafikai shida. Ko wannensu ya rufe fuskarsa da fiffike biyu, jikinsa kuma da fiffike biyu, sauran fiffike biyu ɗin kuma, da su yake tashi.
Explore Ish 6:2
7
Ish 6:6
Sa'an nan ɗaya daga cikin talikan ya tashi ya sauko zuwa gare ni, yana riƙe da garwashin wuta wanda ya ɗauko da arautaki daga bagade.
Explore Ish 6:6
8
Ish 6:9
Saboda haka sai ya ce mini in tafi in faɗa wa jama'a wannan jawabi cewa, “Kome yawan kasa kunne da za ku yi, ba za ku fahimta ba. Kome yawan dubawar da za ku yi, ba za ku san abin da yake faruwa ba.”
Explore Ish 6:9
9
Ish 6:10
Sa'an nan ya ce mini, “Ka sa hankalin mutanen nan ya dushe, kunnuwansu su kurunce, idanunsu su makance, har da ba za su iya gani, ko ji, ko fahimta ba. In da za su yi haka mai yiwuwa ne su sāke juyowa gare ni in warkar da su.”
Explore Ish 6:10
Home
Bible
Plans
Videos