1
Ish 30:21
Littafi Mai Tsarki
HAU
Idan kuka kauce daga hanya zuwa dama ko hagu, za ku ji muryarsa a bayanku yana cewa, “Ga hanyan nan, ku bi ta.”
Compare
Explore Ish 30:21
2
Ish 30:18
Duk da haka dai, Ubangiji yana jira ya yi muku alheri. A shirye yake ya yi muku jinƙai, domin a kullum yana aikata abin da yake daidai. Ta wurin dogara ga Ubangiji ake samun farin ciki.
Explore Ish 30:18
3
Ish 30:15
Ubangiji, Allah Mai Tsarki na Isra'ila, ya ce wa jama'a, “Ku komo gare ni a natse, ku dogara gare ni. Sa'an nan za ku zama ƙarfafa ku zauna lafiya.” Amma ba ku yarda ba!
Explore Ish 30:15
4
Ish 30:20
Ubangiji zai sa ku ku sha wahala, amma shi kansa zai kasance tare da ku, ya koya muku, ba za ku ƙara wahalar nemansa ba.
Explore Ish 30:20
5
Ish 30:19
Ku jama'ar da suke zaune a Urushalima ba za ku ƙara yin kuka ba. Ubangiji mai juyayi ne, sa'ad da kuka yi kuka gare shi neman taimako, zai amsa muku.
Explore Ish 30:19
6
Ish 30:1
Ubangiji ya yi magana, ya ce, “Waɗanda suke mulkin Yahuza sun shiga uku, domin sun tayar mini. Suna aiki da shirye-shiryen da ba ni ne na yi ba, suka sa hannu a kan yarjejeniya gāba da nufina. Suna ta aikata zunubi a kan zunubi.
Explore Ish 30:1
Home
Bible
Plans
Videos