1
Gal 6:9
Littafi Mai Tsarki
HAU
Kada mu yi sanyi da yin aiki nagari, don za mu yi girbi a kan kari, in ba mu karai ba.
Compare
Explore Gal 6:9
2
Gal 6:10
To, saboda haka, in hali ya yi, sai mu kyautata wa kowa, tun ba ma waɗanda suke jama'ar masu ba da gaskiya ba.
Explore Gal 6:10
3
Gal 6:2
Ku ɗauki wahalar juna, ta haka za ku cika shari'ar Almasihu.
Explore Gal 6:2
4
Gal 6:7
Kada fa a yaudare ku, ai, ba a iya zambatar Allah. Duk abin da mutum ya shuka, shi zai girba.
Explore Gal 6:7
5
Gal 6:8
Wanda ya yi shuka a kwaɗayin son zuciyarsa, ta wurin son zuciya zai girbi ruɓa. Wanda ya yi shuka a Ruhu, ta wurin Ruhu zai girbi rai madawwami.
Explore Gal 6:8
6
Gal 6:1
Ya ku 'yan'uwa, in an kama mutum yana a cikin yin laifi, ku da kuke na ruhu, sai ku komo da shi a kan hanya da tawali'u, kowa yana kula da kansa kada shi ma ya burmu.
Explore Gal 6:1
7
Gal 6:3-5
Kowa ya zaci shi wani abu ne, alhali kuwa shi ba kome ba ne, ya ruɗi kansa ke nan. Kowa yă auna aikinsa ya gani, sa'an nan ne zai iya gadara da maƙaminsa shi da kansa, ba sai ya gwada kansa da wani ba. Lalle kowa yă ji da kayansa.
Explore Gal 6:3-5
Home
Bible
Plans
Videos