1
Eze 4:4-5
Littafi Mai Tsarki
HAU
“Sai kuma ka kwanta a hagunka, ni kuwa zan ɗora maka muguntar Isra'ilawa. Za ka ɗauki muguntarsu bisa ga yawan kwanakin da za ka kwanta a hagunka. Gama na ɗora maka kwanaki bisa ga shekarun muguntarsu, wato kwana ɗari uku da tasa'in da za ka kwanta. Ta haka za ka ɗauki alhakin muguntar mutanen Isra'ila.
Compare
Explore Eze 4:4-5
2
Eze 4:6
Sa'ad da ka cika waɗannan kwanaki, sai ka sāke kwantawa, kwanciya ta biyu, a damanka kwana arba'in don ka ɗauki alhakin muguntar mutanen Yahuza. Kwana ɗaya a bakin shekara guda.
Explore Eze 4:6
3
Eze 4:9
“Ka kuma ɗauki alkama, da sha'ir, da wake, da waken soya, da gero, da acca, ka haɗa su a kasko ɗaya, ka yi abinci da su. Shi ne za ka ci a kwanakin na ɗari uku da tasa'in da za ka kwanta.
Explore Eze 4:9