Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Sauka, gama jama'arka da ka fito da su daga ƙasar Masar sun ƙazantar da kansu. Sun yi saurin kaucewa daga hanyar da na umarce su. Sun yi wa kansu ɗan maraƙi na zubi, sun yi masa sujada, sun miƙa masa hadaya, sun kuma ce, ‘Ya Isra'ila, wannan shi ne allahn da ya fisshe ka daga ƙasar Masar’ ”