Sa'ad da kuka ci kuka ƙoshi, kuka gina kyawawan gidaje, kuka zauna ciki, garkunanku na shanu da tumaki suka riɓaɓɓanya, azurfarku, da zinariyarku suka ƙaru, sa'ad da dukan abin da kuke da shi ya haɓaka, to, sai ku lura, kada ku ɗaukaka kanku, har ku manta da Ubangiji Allahnku wanda ya fisshe ku daga ƙasar Masar, wato inda kuka yi bauta.