1
M.Sh 4:29
Littafi Mai Tsarki
HAU
Amma idan kun nemi Ubangiji Allahnku a can inda kuke, za ku same shi muddin kun neme shi da zuciya ɗaya, da dukan ranku.
Compare
Explore M.Sh 4:29
2
M.Sh 4:31
Ubangiji Allahnku, Allah mai jinƙai ne. Faufau, ba zai kunyata ku ba, ba kuwa zai hallaka ku ba, ba kuma zai manta da alkawarin da ya rantse wa kakanninku ba.
Explore M.Sh 4:31
3
M.Sh 4:24
Gama Ubangiji Allahnku wuta ne mai cinyewa, shi kuma mai kishi ne.
Explore M.Sh 4:24
4
M.Sh 4:9
“Sai ku lura, ku kiyaye kanku sosai, don kada ku manta da abubuwan da kuka gani da idonku kada kuma su fita a ranku dukan kwanakinku. Ku sanar wa 'ya'yanku da jikokinku da su
Explore M.Sh 4:9
5
M.Sh 4:39
Domin haka, yau sai ku sani, ku kuma riƙe a zuciyarku, cewa Ubangiji shi kaɗai ne Allah a sama da duniya. Banda shi, ba wani kuma.
Explore M.Sh 4:39
6
M.Sh 4:7
“Gama babu wata babbar al'umma wadda allahnta yake kusa da ita kamar yadda Ubangiji Allahnmu yake kusa da mu sa'ad da muka kira gare shi.
Explore M.Sh 4:7
7
M.Sh 4:30
Sa'ad da wahala ta same ku, waɗannan abubuwa kuma suka auko muku nan gaba, za ku juyo wurin Ubangiji Allahnku, ku yi masa biyayya.
Explore M.Sh 4:30
8
M.Sh 4:2
Kada ku ƙara, ko ku rage kome daga cikin abin da na umarce ku, amma ku kiyaye umarnan Ubangiji Allahnku, waɗanda nake umartarku da su.
Explore M.Sh 4:2