Daniyel ya amsa wa sarki, ya ce, “Ba masu hikima, ko masu dabo, ko masu sihiri, ko masu duba, da za su iya su warware wa sarki wannan matsala da ta dame shi. Amma akwai Allah a Sama mai bayyana asirai, shi ne ya sanar wa sarki Nebukadnezzar da abin da zai faru a kwanaki masu zuwa. Mafarkinka da wahayinka waɗanda suka zo cikin tunaninka, sa'ad da kake kwance bisa gadonka ke nan.