“ ‘Je ka wurin jama'ar nan, ka ce,
Za ku ji kam, amma ba za ku fahimta ba faufau,
Za ku gani kuma, amma ba za ku gane ba faufau.
Don zuciyar jama'ar nan ta yi kanta,
Sun toshe kunnuwansu,
Sun kuma runtse idanunsu,
Wai don kada su gani da idanunsu,
Su kuma ji da kunnuwansu,
Su kuma fahimta a zuciyarsu,
Har su juyo gare ni in warkar da su.’